Babba Kaita ya taya al’ummar Katsina murnar cika shekaru 39 da ƙirƙira

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Sanata Ahmad Babba Kaita, ya taya al’ummar jihar murnar cika shekaru 39 da kafuwarta, tare da yin kira da a yi addu’ar Allah ya kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro, talauci da sauran ƙalubalen da jihar ke fuskanta.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da mai magana da yawun ɗan takarar Abubakar Ahmed ya fitar yayin da Jihar Katsina ke bikin cika shekaru 39 da kafuwarta, yana mai cewa duk da cewa ranar cikar jihar shekaru 39 abin farin ciki ce, akwai buƙatar yin tunani kan halin da al’ummar jihar ke ciki.

Ya ce rashin tsaro, talauci da matsin tattalin arziki na daga cikin manyan matsalolin da al’ummar Katsina ke fuskanta, yana mai cewa ya kamata a yi addu’a tare da neman mafita daga Allah domin samun sauƙi da zaman lafiya.

Kaita ya kwatanta Jihar Katsina da mutum mai shekaru 39, wanda a irin wannan lokaci ya kamata ya kasance mai cikakken ƙarfi da dogaro da kansa.

Sai dai ya ce duk da irin gudunmawar da wasu shugabannin baya suka bayar wajen ci gaban jihar, a halin yanzu al’umma na fuskantar tsoron hare-haren ’yan bindiga da matsin rayuwa.

A yayin da zaɓen 2027 ke ƙara kusantowa, Kaita ya yi kira ga al’ummar jihar da su sake nazari kan irin shugabannin da za su zaɓa, yana mai cewa jam’iyyar ADC na son kawo tsarin shugabanci da take cewa zai mayar da hankali kan sauye-sauye da haɗa kan al’umma wajen ci gaban Jihar Katsina.

By ukarofi