‘Yan sanda a sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane a Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa sun daƙile wani shiri na garkuwa da mutane tare da kama wasu mutum huɗu da ake zargi da shirya kashe wanda za su sace bayan sun karɓi kuɗin fansa.

Rundunar ta kuma sanar da kama wasu mutum biyu dake da alaƙa da kisan da ya shafi ƙungiyar asiri da aka samu a Lafia da safiyar Laraba.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma ya aikawa Nigerian Tribune a ranar Laraba a Lafia.

A cewar sanarwar jami’an sashen leƙen asiri na Jihar (SID) a Lafia bisa sahihan bayanan sirri kan haɗa baki da yunƙurin garkuwa da mutane, sun gano shirin garkuwar tare da ƙaddamar da bincike na sirri.

Nansel ya ce binciken ya kai ga kama mutum huɗu, dukkansu mazauna gundumar Adudu a ƙaramar hukumar Obi. Waɗanda ake zargin sune Yahaya Musa, Likita Adamu, Riga Abdullahi da Saidu Alhaji Gari.

Yace binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun kammala shirin sace wani Alhaji Ibrahim Abdullahi, wanda aka fi sani da Alhaji Na’iye.

“An gano shirin kafin a aiwatar da shi,” in ji Nansel, inda ya ƙara da cewa an kama biyu daga cikin waɗanda ake zargin ne a ranar 19 ga Satumba, yayin da aka kama na uku da na huɗu a ranakun 22 da 23 ga Satumba.

Kakakin ‘yan sandan ya ƙara da cewa yayin da ake yi musu tambayoyi, waɗanda ake zargin sun amsa laifin tare da amincewa cewa sun shirya kashe wanda za su sace bayan sun karɓi kuɗin fansa.

Yace an miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jiha (SCID), Lafia, domin cigaba da bincike da gurfanar da su a gaban kuliya.

A wani labari mai alaƙa Nansel ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 6:00 na safiyar ranar 24 ga Satumba, cewa an ga wani mutum kwance cikin jini a bayan yankin Eji-World a Lafia.

Ya ce DPO na Ombi 1 Division a Lafiya ya jagoranci tawaga zuwa wurin inda suka tarar da wani matashi ɗan shekara 26 da aka bayyana sunansa da Venus, ɗan asalin jihar Benue.

“An garzaya da wanda abin ya shafa zuwa babbar asibitin koyarwa ta tarayya da ke Lafia, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa,” in ji shi.

Nansel yace binciken farko ya nuna cewa maharan sun je neman abokin mamacin ne, wato Joseph Friday Oluyemi na titin Maisoti a Lafia, wanda a baya ya ba da rahoton cewa yana karɓar barazana daga ‘yan ƙungiyar asiri.

Yace an kama wasu mutum biyu, Friday Joshua da ThankGod Auta Vincent, dangane da kisan, yayin da ake ƙoƙarin cafke sauran waɗanda suka gudu. Ya ƙara da cewa an ajiye gawar a ɗakin ajiye gawa na asibitin domin gudanar da binciken gawa.

A halin yanzu kwamishinan ‘yan sanda, CP Shetima Jauro Mohammed ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike na ƙwarai kan dukkan lamuran biyu kuma ya tabbatar da cewa za a hukunta duk masu hannu a ciki.

Kwamishinan ya kuma buƙaci mazauna yankin da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wata mu’amala da ake zargi ga ‘yan sanda cikin gaggawa.

By ukarofi

Leave a Reply