Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya buƙaci masu zuba jari masu zaman kansu su ƙara shiga ayyukan da za su taimaka wajen raya jihar, musamman a fannonin noma, sarrafa amfanin gona, sufuri, kiwon lafiya da samar da ayyukan yi.
Gwamnan ya bayyana haka ne a taron ASIS Global Action Forum da aka gudanar a New York, a wani ɓangare na taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 (UNGA 81).
Ya ce Katsina ta samu tallafin ayyukan raya ƙasa da dama, ciki har da sama da dala miliyan 430 daga Bankin Duniya, da kuma dala miliyan 30 daga AfDB da dala miliyan 60 daga Islamic Development Bank.
Gwamna Raɗɗa ya ce gwamnati za ta samar da yanayin da zai bai wa masu zuba jari damar bunƙasa kasuwanci ta hanyar tabbatar da manufofi, inganta kwangiloli, da kuma tabbatar da gaskiya da tsaro.
Ya kuma buƙaci masu zuba jari su shiga cikin ayyuka tun daga matakin tsara su, domin samar da ayyuka masu ɗorewa da fa’ida ga al’umma.
