
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya yi alla-wadai da gayyatar da Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL) ya yi masa zuwa matatar Fatakwal inda ya ce hakan babu girmamawa.
NNPCL ta hannun Kakakinsa Olufemi Soneye ya gayyaci tsohon Shugaban ƙasar zuwa ziyarar gani da ido a matatun Fatakwal da Warri.
Hakan na zuwa ne a lokacin da tsohon shugaban ƙasar ya hakaito yadda aka gaza sayar da rijiyoyin mai a Nijeriya a baya, kamar yadda ya faɗa a wata hira da tashar ‘channels’.
Obasanjo ya bayyana takaicinsa kan yadda aka gaza gudanar da matatun yadda ya kamata, ya na mai cewa duk da kashe-kashe mai yawa da aka yi tun daga shekarar 2007, babu wani sakamako mai kyau.
Ya kuma bayyana yadda magajinsa marigayi Umaru Musa Yar’adua ya ƙi karɓar Dala miliyan 750 daga Shugaban rukunin kamfanin Ɗangote, Aliko Ɗangote don gudanar da matatun Fatakwal da Kaduna, ya na mai cewa Ɗangote zai kula da su sama da yadda gwamnati za ta yi.
Saidai NNPCL, Kamar yadda Kakakin nasa ya bayyana, ya ce matatun su na aiki yadda ya kamata.
A lokacin da jami’in yaɗa labaran Obasanjo, Kehinde Akinyemi ke magana game da lamarin ya ce har zuwa ranar Alhamis 2 ga watan Junairu, babu wata gayyata ta musamman zuwa ga mai gidan nasa.
