‘Babu jami’in girki da aka kama’, inji Fadar Shugaban Ƙasa yayin watsi da zargin sanya wa Tinubu guba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen Soshiyal Mediya da ke zargin an kama wasu ma’aikatan dafa abinci na fadar bisa zargin su da kitsa makircin sanya wa Shugaba Bola Tinubu guba, tana mai bayyana hakan a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a.

Rahotanni sun bayyana cewa fadar ta yi bayanin ne a sa’ilin da wani bidiyo da ke zargin kama jami’in da kitsa makircin sanya wa shugaban ƙasar ya karaɗe kafafen.

A bidiyon, an jiyo wata murya da ke bayyana yadda ake gudanar da wasu ayyuka a fadar da kuma bayanin zargin kitsa makircin, wanda aka ce an gano haka ne sakamakon samun waɗansu bayanai na sirri.

Bidiyon ya kuma bayyana yadda jami’an ‘yan sanda suka gaggauta kama wanda ake zargi tare da tafiya da shi komar hukumar domin gudanar da bincike akansa.

Tuni dai hukumomin da ke kula da fadar shugaban ƙasar suka hanzarta fayyace wa al’umma yadda al’amarin yake domin kauce wa shiga ruɗani.

Faifan ya kuma bayyana cewa ana gudanar da bincike a kai duk da cewa zargi ba tabbatar da al’amari ba ne kai-tsaye.

Da yake tsokaci akan al’amarin, Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ta kafar X, ya yi watsi da rahotan, inda ya bayyana shi a matsayin “bogi”.

A cewarsa, “Babu jami’in girki na Aso Rock da aka kama. Babu jami’in girkin Aso Rock da ya yi yunƙurin sanya wa Shugaba Tinubu guba. Don Allah ku yi watsi da wannan labarin bogin da aka yaɗa a wannan bidiyon.”

Ya bayyana haka ne da nufin kore dukkan wani zargi da kuma sake tabbatar wa al’umma cewa babu wani aikin saɓa wa doka ko kame da aka yi acikin fadar.

By Babaji