
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani ɗan Nijeriya da ya bar ƙasar domin neman waje mai tsaro ya bayyana kaɗuwarsa sakamakon tsintar kansa a yankin Gabas ta Tsakiya da ke fama da rikici tsakanin ƙasashe.
Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, an ga mutumin yana bayanin yadda ya bar Nijeriya ya dawo Bahrain, inda a lokacin da ya yi yunƙurin fita daga kasarne sai hare-haren makamai masu linzami suka yi ƙamari da ya haɗa da ƙasar Iran.
“Na bar ƙasata Nijeriya saboda ana harbin bindiga a can. Abin da suke harbawa a ƙasata kaɗai ita ce AK-47. Yanzu ina Bahrain kuma suna harba makamai masu linzami. Ban ma san wanne ne ya fi sauƙi ba”, inji shi yayin da yake gudu.
Mutumin bai bayyana ainihin inda yake ba a lokacin da ake luguden wutar, saidai kalaman nasa sun nuna yadda masu neman mafaka a yankin gabas ta tsakiya suk cikin mawuyacin hali.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da faɗa tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila ya ƙamari bayan Amurka ta farmaki Iran a ranar 28 ga Fabrairu.
