Daga UMAR GARBA a Katsina
Kungiyar Dattawan Jihar Katsina ta nuna adawarta game da sauya wa wasu hukumomin gwamnati mazauni da Gwamnatin Tarayya ke yi a halin yanzu, ciki har da dauke aikin fadada filin jirgin sama na Malam Umaru Musa ‘Yar’adua dake Katsina wanda gwamnatin tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ta bada kwangilar aikin don inganta shi.
Rahotanni sun bayyana cewar Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, ta bayyana aniyarta na dauke wasu rassa na Babban Bankin Nijeriya daga Abuja zuwa Jihar Lagos da kuma sauya wa hedikwatar Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN) zuwa Lagos.
A dalilin haka ne kungiyar dattawan ta kira taron manema labarai, inda ta bayyana cewar ta samu wani labari dake nuna cewar sauye-sauyen za su shafi aikin filin jirgin sama na Katsina, don haka ne suka gargadi shugaban kasa da ya fasa aniyar tasa ko kuma ya rasa kuri’un al’umar jihar a zaben 2027.
Sakataren kungiyar, Aliyu Muhammed, ya bayyana cewar dan kwangilar ya rubuta wa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Kiyamo, wasika inda yake neman a ba shi dama ya dauke aikin filin jirgin sama na Katsina zuwa Kudu.
Muhammed ya ce, wadanda suka ba wa Shugaban Kasa shawarar dauke reshen CBN da hedikwatar hukumar FAAN zuwa Legas makiyan Shugaban Kasar ne wadanda ke kokarin tarwatsa hadin kan kasar nan.
“Saboda haka, muna kira ga Shugaban Kasa matukar yana son kuri’un al’umar Arewa a zaben Shekarar 2027 ya sake mayar da wadannan hukumomi wuraren da suke tun asali. Duk wanda ya ba shi wannan shawarar maqiyin Kasar nan ne,” inji shi.
Kazalika, Kungiyar ta soki lamirin Ministan Birnin Tarayya, Nwesom Wike, kan zaman tattaunawa da ya yi da jakadan Kasar Isra’ila.
Kungiyar ta ce matukar shugaba Tinubu bai dauki yankin arewacin kasar da muhimmanci ba musamman bangaren samar da tsaro da inganta rayuwar al’umar yankin, to fa, ya manta da samun goyon bayansu a manyan zabuka masu zuwa.
