Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ma’aikatan jihar Katsina, Malam Falalu Bawale ya faɗi haka ga manema labarai a Katsina.
Ya bayyana cewa shi wannan shirin gina gidaje tare da haɗa su da harkokin noma da kiwo (aquaculture) babu kobon gwamnatin Katsina a ciki.
Alhaji Bawale ya ce gwamnati ta rattaba hannu ne kan yarjejeniyar fahimta (MoU), da Cosmos Investment Nigeria Limited, tare da haɗin gwiwar ma’aikatar gidaje ta tarayya, gwamnatin Jihar Katsina da CESA Investment Limited, domin gina kusan gidaje 3750 a garuruwan kankiya da Raɗɗa domin shirin noma da kiwo.
Ya ce, waɗannan kamfanoni da ke zaune a ƙasar Amurka su za su gina gidajen,ita kuma gwamnatin jihar Katsina za ta basu filayen gini da kariyar aikin.
Ya jaddada cewa shirin zuba jari ne da nufin samar da ayyukan yi, bunƙasa tattalin arziki da ƙarfafa matasa, yana mai cewa gwamnatin jihar ba za ta kashe ko sisi ba a aikin.
“Gwamnatin jihar za ta ware fili a wuraren da aka zaɓa, yayin da mahalarta shirin za a zaɓo daga ƙananan hukumomi 34 na jihar da za su shiga aikin noma da kiwon ƙarƙashin kulawar kamfanin da ya zuba jarin,”inji Bawale.
A cewar sa za a horar da mahalarta kan dabarun noma na zamani, za a rika biyansu albashin wata-wata, sannan a ƙarshen shirin za a mallaka musu gidajen da suka zauna muddin sun cika sharuɗɗan shirin.
“Da zarar an kammala shirin, waɗanda suka yi aiki yadda ya kamata za su mallaki gidajen har abada,” in ji Alhaji Bawale.
Babban manajan hukumar gidaje ta Jihar, Dakta Aliyu Rabi’u Kurfi, a nasa bayani ya tabbatar da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da kuma ministan hidaje birane, Ahmed Musa Dangiwa suka amince wa kamfanin da ya gina irin waɗannan gidajen noma a Katsina.
“Ba da fili da kuma garanti abu ne da doka da al’ada suka tanada, kuma ba ya nufin fitar da kuɗin gwamnati,” in ji shi.
Ya musanta duk wani zargi na cewa an umurci wasu ma’aikatu ko hukumomi su fitar da kuɗi domin aikin.
A nasa jawabin, Adam Ya’u,na Aspire USA Incorporated masu gina gidajen ya bayyana aikin a matsayin na farko irinsa a Yammacin da zai ci kuɗi Naira biliyan 155.
Ya ce an zaɓi Jihar Katsina ne bisa Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda shugaban ƙasa ya amince da aiwatar da aikin a shiyyoyi shida na ƙasar, inda Katsina ta fito daga Arewa maso Yamma.
Ya’u ya bayyana cewa Kankiya na daga cikin wuraren da aka fara aikin saboda kusancinta da filayen jiragen sama na Kano, wanda hakan zai sauƙaƙa fitar da amfanin noma da kiwo zuwa ƙasashen waje.
Sai garin Raɗɗa da ya ce tafi kusanci da kankiya
Malam Ya’u,ya bayyana amfanin aikin da ya ce zai taimaka wajen rage ƙauracewar matasa daga karkara zuwa birane, samar da ayyukan yi, da bunƙasa rayuwar al’umma ba tare da la’akari da shekarun mutum ko matakin ilimi ba.
An kammala taron da kira ga kafafen yaɗa labarai da su taimaka wajen wayar da kan al’umma da kawar da duk wani shakku ko ruɗani game da aikin.
Kafin wannan ƙarin haske, mutane su na ta ƙorafe ƙorafe kan yadda gwamnatin Katsina za ta ware biliyoyin Naira akan wannan aiki,to sai a bayanin da tayi a bakin shugaban ma’aikatan jihar, gwamnatin Katsina ba za ta kashe ko kobo ba a wannan aikin gina gidaje.
