Babu mahalukin da zai hana rantsar da Tinubu – Sarkin Musulmi

Daga BASHIR ISAH

Mai Alfamar Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkar Muslunci a Nijriya, (NSCIA), Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce babu wani mahalukin da zai dakatar da rantsar da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya zuwa ranar 29 ga Mayu.

Basaraken ya bayyana hakan ne sa’ilin da yake jawabi a wajen wani taro da Bankin Duniya ya shirya a Abuja ranar Laraba.

Ya ce maimakon ƙoƙarin dagula wa rantsawar lissafi kamata ya yi ’yan Nijeriya su himmantu da yi wa gwamatin Tinubu addu’a da fatan nasara.

A cewarsa: “Dole a samu canji, saboda nan da ‘yan kwanaki ko makonni za a samu sabuwar gwamnati; wace irin gudunmawa za mu bai wa gwamnatin don samun daidaito?

“Ko mutum ya so, dole hakan za ta kasance, sabuwar gwamnati za ta shigo ya zuwa ran 29 ga Mayu, don haka me za mu yi da ya wuci addu’a, don kuwa mun yi imani da Ubangiji, mun yarda cewa Shi ke bayarwa, kuma Shi ke karɓewa.

“Bayan nan kuma sai me? Me za mu yi don taimaka wa gwamnatin samun daidaito wajen ciyar da ƙasa gaba?”

Daga nan, Sarkin Musulmin ya yi kira ga ’yan NIjeriya da su haɗe kai sannan a yi aiki tare don cigaban ƙasa.