
Adeniyi Adeyemi, wanda ke iƙirarin cewa shi ne Darakta Janar na abin da ya kira Hukumar Bunƙasa Zuba Jarin Ƙasashen Waje ta Fadar Shugaban Ƙasa (PFIPC), ya rubuta buɗaɗɗiyar wasiƙa ga Shugaba Bola Tinubu inda ya buƙaci a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin binciken takaddamar da ta dabaibaye hukumar.
A cewarsa, ya kamata kwamitin ya haɗa da wakilan Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), Amurka, Birtaniya, Tarayyar Turai, ECOWAS, AU, ƙungiyoyin fararen hula da masu sa ido na ƙasa da ƙasa domin tabbatar da gaskiya da amincewar jama’a.
Rahotanni sun bayyana cewa, Adeyemi ya ce ba zai amince ICPC ita kaɗai ta gudanar da binciken ba, duk da cewa Shugaba Tinubu ya umarci hukumar ta binciki zarge-zargen da suka shafi PFIPC.
Ya yi iƙirarin cewa idan aka kafa kwamitin mai cin gashin kansa, zai gabatar da hujjoji da takardun da ya ce za su tabbatar da matsayinsa, tare da zargin cewa miƙa kansa ga jami’an tsaro a halin yanzu na iya jefa rayuwarsa cikin haɗari.
Saidai a ɗaya ɓangaren, Fadar Shugaban Ƙasa ta sha nanata cewa babu wata hukuma mai suna PFIPC a tsarin gwamnatin tarayya.
Haka kuma masu gabatar da ƙara sun tuhumi Adeyemi da ƙirƙira takardun gwamnati da suka haɗa da wasiƙar naɗi daga shugaban ƙasa da wasu takardun hukuma, zarge-zargen da yake ci gaba da musantawa yana mai cewa naɗin nasa sahihi ne.
Adeyemi ya kuma yi zargin cewa wasu manyan jami’an gwamnati sun hana shi gudanar da aikinsa, yayin da ya sake jaddada cewa idan akwai saɓani kan lamarin, kotu ce kaɗai ya kamata ta yanke hukunci.
A nata ɓangaren, gwamnati ba ta amince da iƙirarin nasa ba, kuma ana cigaba da shari’ar da ake yi masa a kotu kan zarge-zargen da ake masa.
An rawaito cewa, yayin da ake cigaba da takaddamar PFIPC, hukuncin kotu da sakamakon binciken hukumomin da abin ya shafa ne za su tabbatar da gaskiyar zarge-zargen da ɓangarorin biyu ke yi.
