Bai kamata mu yi saurin mantawa da gudunmawar Kaunda ba – Buhari

Daga AISHA ASAS

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana tsohon Shugaban Ƙasar Zambiya, Kenneth Kaunda, a matsayin “Ɗaya daga cikin manyan shugabannin Afirka da na duniya baki ɗaya da ke ƙaunar ƙasarsa da mutanensa sosai.

Buhari ya ce labarin rasuwar Kaunda ya kaɗa shi matuƙa saboda sanin irin gudunmawar da ya bai wa ƙasarsa Zambiya da ma Afirka baki ɗaya a halin rayuwarsa.

A sanarwar da ta tafito ta hannun mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, “Ba za mu yi saurin manta gwagwarmayar Kaunda ba wajen ƙwato wa Zambjya ‘yanci daga Afirka ta Kudu da kuma tsohuwar Rhodesia.”

Buhari ya ce marigayin na ɗaya daga cikin waɗanda suka sha gwagwarmaya wajen raba Afirka da mulkin mallaka, kuma ya yi hakan ne da gaskiya ba tare da nuna wani son kai ba.

Bauhari ya miƙa ta’aziyyarsa da ta ƙasarsa Nijeriya, ga iyalan marigayin da ma al’ummar Zambiya baki ɗaya dangane da rashin.