Ban taɓa ko kwana ɗaya a gidan yari ba lokacin da aka tsare ni, na zauna a otal ne – Bobrisky

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shahararren ɗan daudun nan mai suna Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky, ya bayyana cewa bai taɓa kwana ɗaya a gidan yari ba bayan da aka same shi da laifi kuma aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari bisa laifin wulaƙanta Naira a watan Afrilun 2024.

Ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan murya da wani fitacce, ɓeryDarkMan ya fitar a daren Talata.

Kamar yadda muryar ta bayyana, Bobrisky ya kuma amince cewa ya biya wasu jami’an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) kuɗi har naira miliyan 15 kan tuhumar da ake masa na halasta kuɗaɗen haram.

A cikin faifan muryar, ɗan daudun ya kuma yi iƙirarin cewa bayan da aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na watanni shida, “mahaifinsa” ya yi kira ga hukumomin gidan yarin, waɗanda suka ba shi masauki a maimakon gidan yari.

Ya ƙara da cewa don ɓoye tsarin an umarce shi da kada ya fito daga otal ɗin har tsawon zaman gidan yari kuma kada ya sanar da kowa.

Ya kasance a watan Afrilun 2024, Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) ta kama shi kuma ta tsare shi a Legas kuma an yanke masa hukuncin watanni shida ba tare da zaɓin biyan tara ba bisa laifin wulaƙanta Naira.

An sake shi daga gidan gyaran hali na ƙirikiri a ranar 5 ga Agusta, 2024, bayan ya shafe sama da watanni huɗu a cikin hukuncin da aka yanke masa na watanni shida.

By ukarofi