Muna zaune lafiya tare da sauran ƙabilu a Legas – Mansir Sani

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Sarkin al’ummar Hausawa mazauna Unguwar Odugunya barak ta ƙaramar Jukumar Ikorodu dake cikin garin Legas, Alhaji Mansir Sani ɗan asalin ƙaramar hukumar Faskari dake cikin jihar Katsina, ya bayyana cewar su da sauran al’ummar Hausawa mazauna unguwar Ikorodu ta jihar  Legas suna cigaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da sauran ƙabilu mazauna yankin na Legas gaba ɗaya.

Sarkin Hausawan na Pdugunya Barak Alhaji Mansir Sani ya yi wannan tsokaci ne jim kaɗan bayan kammala taronsu da waɗansu sarakunan Yarabawa wanda suka saba yi a duk ƙarshen mako domin tattaunawa bisa kan abubuwan da za su ƙara zaman lafiya da fahimtar juna a tsakaninsu.

Sarkin ya cigaba da yi wa Jaridar Blueprint Manhaja a Legas fashin baƙi dangane da al’amarin inda ya ci gaba da cewa,”haƙiƙa a daidai wannan lokacin al’ummar Hausawa mazauna jihar Legas suna cigaba da samun zaman lafiya da fahimtar juna tare da sauran ƙabilu mazauna jihar ta Legas idan aka yi la’akari da irin yadda ‘yan Arewacin Nijeriya mazauna jihar Legas suke cuɗanya da junansu da kuma tafiya kafaɗa da kafaɗa a tsakaninsu da sauran ƙabilun mazauna jihar ta Legas gaba ɗaya.”

Ya ƙara da cewa akan hakan yake ƙara shawartar ƙabilun guda biyu, wato ƙabilar Hausawa da ta Yarabawa da sauran ƙabilu mazauna yankin na Legas da su ƙara ƙoƙari a wajen nemo hanyoyin cigaba samun zaman lafiya domin ciyar da ƙasar nan gaba.

Haka zalika ya cigaba da jawo hankulan ‘yan arewacin Nijeriya mazauna jihar ta Legas da su cigaba da haɗa kawunan junansu tare da bin dokokin gwamnati jihar Legas domin kwalliya ta cigaba da biyan kuɗin sabulu kamar yadda ya kamata.

Sannan ya cigaba da nuna rashin jin daɗin sa dangane da iftila’in ambaliyar ruwan da ya faru a garin Maiduguri, ya ce da fatan Allah Ubangiji ya kare faruwar irin wannan al’amari anan da shekarun gaba masu zuwa. Ya ce bisa ga haka yake isar da saƙon jaje fadar mai martaba Shehun Borno Alhaji Garbai Shehu da Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum dangane da faruwar wannan al’amari, da fatan Allah Ubangiji ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu kuma ya mayar wa waɗanda suka yi asarar gidajensu da mafificin abinda suka rasa.

By ukarofi