Ban yi kuskuren ɗaukar ka mataimaki ba – Tinubu ga Shettima yayin zagayowar ranar haihuwarsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A wani yanayi na karramawa, Shugaba Bola Tinubu ya taya Mataimakinsa, Kashim Shettima murnar cikar sa shekaru 59 a duniya.

Tinubu ya bayyana Shettima a matsayin mataimaki mai biyayya da ya cancanci a dogara da shi wajen sauke nauyin hidimta wa al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.

A sanarwar da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce bai yi kuskure ba wajen zaɓar Shettima a matsayin abokin tafiyarsa, wanda kuma ya zama mataimaki a gare shi wajen shugabantar Nijeriya.

Ya jinjina wa jajircewar Shettima da ƙoƙarinsa wajen samar da haɗin kai da ci-gaba masu ɗorewa a ƙasar tun daga lokacin da suka fara aiki tare.

Haka kuma Shugaba Tinubu tunatar da hidimar da Shettima ya yi a matsayinsa na gwamna har sau biyu a Jihar Borno da zamansa sanata daga bisani, ganin yadda ya jajirce wajen sauke nauyin da ya ɗauka duk da ƙalubalen da ya fuskanta.

Har’ilayau, Shugaba Tinubu ya yaba wa gudumawar mataimakin nasa a mataki na ƙasa a fannonin ci-gaban dimukraɗiyya, shugabanci da harkar tattalin arziƙin ƙasa.

By Babaji