Ban zo don kawar da ma’aikata ba, cewar ministar AI na Albaniya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sabuwar mutum-mutumi ta fasahar AI da aka ƙirƙira kuma aka naɗa muƙamin minista a ƙasar Albaniya ta yi jawabi a karon farko a gaban majalisar dokokin ƙasar.

A ranar Alhamis ce dai ministan ya bayyana gaban majalisar, inda ya kare rawar da zai taka a gwamnati, yana mai cewa, “Ban zo don na maye gurbin mutane ba, sai dai don taimaka musu.”

Wannan minista ta AI wacce aka sanya mata suna Diella, ma’ana “rana” a harshen Albaniya, ita ce ministar gwamnati ta farko a duniya da aka ƙirƙira ta hanyar fasahar AI.

Firaministan Albania, Edi Rama, ne ya naɗa shi a makon da ya gabata.

A cikin wani faifan bidiyo da aka nuna a majalisa, Diella ta bayyana a matsayin mace sanye da kayan gargajiya na Albaniya, inda ta ce: “Wasu sun ce ba na kan dokar kundin tsarin mulki saboda ni ba mutum ba ce.”

Diella ta ƙara da cewa: “Bari in tunatar da ku, babban hatsarin da ke tattare da kundin tsarin mulki ba na injuna ba ne, na masu mulki ne.”

A makon da ya gabata, Firaminista Rama ya bayyana cewa Diella za ta kula da dukkan al’amuran kwangiloli na gwamnati, domin tabbatar da cewa an kawar da cin hanci gaba ɗaya, kuma duk kuɗaɗen gwamnati da aka sanya a cikin tsarin kwangila za su kasance a bayyane.

An ƙaddamar da Diella a watan Janairu a matsayin mataimakiyar fasahar AI da ke taimaka wa jama’a wajen amfani da dandalin e-Albania, wanda ke bayar da takardu da ayyuka na gwamnati.

By ukarofi