Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bankunan Nijeriya sun samu jimillar Naira biliyan 209.18 daga cajin kuɗaɗen kula da asusun kwastomomi, wato Account Maintenance Charges, a watanni ukun farko na shekarar 2026, lamarin da ya nuna ƙarin kaso 14.07 cikin ɗari idan aka kwatanta da Naira biliyan 183.37 da suka samu a daidai wannan lokaci a shekarar 2025.
Wani nazari da aka gudanar kan rahotannin kuɗaɗen da bankuna 11 da aka jera a Kasuwar Hannayen Jari ta Nijeriya (NGɗ) suka fitar ya kuma nuna cewa kuɗaɗen shiga daga kuɗaɗen hidima da kwamitocin gudanarwa, wato Fees and Commissions, sun haura zuwa Naira biliyan 984.47 a rubu’in farko na shekarar 2026, daga Naira biliyan 866.30 a shekarar da ta gabata, wanda ke nuna ƙaruwa da kaso 13.64 cikin ɗari.
Nazarin ya shafi bankuna 11 daga cikin bankuna 13 da ke kasuwar hannayen jari, yayin da FCMB Group da Unity Bank ba su fitar da rahotanninsu na wannan lokaci ba.
Bisa ga ƙa’idojin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya tanada kan cajin da bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi ke yi, kuɗin kula da asusu ana karɓar su ne kawai daga masu asusun ajiyar kuɗi na kasuwanci (Current Account). Wannan tsari ya maye gurbin tsohon tsarin Commission on Turnover (COT) domin taimaka wa bankuna wajen biyan kuɗin gudanar da asusun kwastomomi masu amfani da asusun su akai-akai.
Rahoton ya nuna cewa Zenith Bank ne ya fi samun kuɗaɗen kula da asusu a tsakanin bankunan da suka bayyana wannan kaso kai tsaye, inda ya tara Naira biliyan 25.07 a cikin watanni ukun farko na shekarar.
Sai kuma Ecobank Transnational Incorporated (ETI) wanda ya samu Naira biliyan 118.06 daga kuɗaɗen sarrafa kuɗi da makamantansu, waɗanda ake kallon su a matsayin mafi kusa da kuɗin kula da asusu.
Sauran sun haɗa da: Access Holdings – Naira biliyan 16.68, Guaranty Trust Holding Company (GTCO) – Naira biliyan 15.12, United Bank for Africa (UBA) – Naira biliyan 13.26, Ecobank Ya Fi Kowa Samun Kuɗin Hidima.
A bangaren jimillar kuɗaɗen shiga daga hidimomi da kwamitoci, Ecobank ce ta zo ta farko da Naira biliyan 237.80, sai:
Access Holdings – Naira biliyan 205.03. UBA – Naira biliyan 124.07, First Holdco – Naira biliyan 96.12, Zenith Bank – Naira biliyan 84.79, GTCO Ta Fi Kowa Saurin Haɓaka.
A cikin bankunan da suka bayyana kuɗin kula da asusu kai tsaye, GTCO ta samu mafi girman haɓaka, inda kuɗaɗen suka tashi daga Naira biliyan 10.63 zuwa Naira biliyan 15.12, wanda ke nuna ƙaruwa da kaso 42.15 cikin ɗari.
Haka kuma: Sterling Financial Holdings – ƙaruwa da kashi 38.31, Wema Bank – ƙaruwa da kashi 31.30, Zenith Bank – ƙaruwa da kashi 30.81, UBA – ƙaruwa da kashi 27.65.
Sai dai ba dukkan bankuna ne suka samu ci gaba ba. Fidelity Bank ta samu raguwa da kashi 2.52, yayin da Stanbic IBTC Holdings ta samu raguwa da kashi 4.98 a kuɗaɗen da suka shafi mu’amalar asusu.
