Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani sabon yanayi na fargaba ya mamaye al’umma a wata ƙaramar Hukuma ta Jihar Borno bayan da mayaƙan Boko Haram suka yi garkuwa da matafiya 13, ciki har da jariri mai wata bakwai, a kan hanyar Biu zuwa Damaturu ta yankin Kamuya.
A cewar jaridar Blueprint ‘yan ta’addan sun tare wasu motocin Golf Wagon guda biyu da ke ɗauke da fasinjoji a kan hanyar, inda suka yi awon gaba da matafiyan zuwa wani wuri da ba a sani ba.
An kuma ruwaito cewa iyalan waɗanda aka sace sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Borno, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙara ƙaimi wajen ceto ‘yan uwansu tare da dawo da su gida lafiya.
A cikin wata sanarwa da suka fitar, iyalan sun bayyana cewa suna cikin tsananin damuwa, fargaba da rashin sanin halin da waɗanda aka sace suke ciki tun bayan faruwar lamarin.
Sanarwar ta ce: “Iyalan waɗanda aka sace na kira ga gwamnati, hukumomin tsaro, ƙungiyoyin agaji da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace domin ceto matafiyan da aka yi garkuwa da su tare da tabbatar da sun dawo gida lafiya.”
Lamarin ya sake jaddada ƙalubalen tsaro da ke ci gaba da addabar wasu sassan Arewa maso Gabashin Nijeriya, musamman a Jihar Borno, inda hare-haren Boko Haram ke ci gaba da barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
