Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani Bafulatani da ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane ya bayyana cewa, yawancin masu aikata garkuwa da mutane a Nijeriya ba Fulani ne ’yan asalin ƙasar ba, sai dai wasu daga ƙasashen maƙwabta, musamman daga yankin ƙasar Chadi.
A cikin rahoton da aka samu daga jaridar IntelRegion, mutumin ya bayyana hakan ne yayin da yake ba da labarin irin azabar da ya sha a hannun masu garkuwa da shi, inda ya ce ya kwashe watanni a tsare kafin daga bisani a sake shi.
Ya ce, a duk lokacin da yake tsare, ya lura cewa daga cikin ’yan bindigar da suka riƙe shi babu wanda ya fito daga Fulani ’yan Nijeriya, yana mai zargin cewa yawancinsu daga ƙasashen waje ne suka shigo cikin ƙasar.
Ya ce, “Ni Bafulatani ne. Ba mu yin garkuwa da mutane domin mu na da sana’o’inmu da muke rayuwa da su. Ba ma roƙon Allah ya ba mu damar cutar da ’yan Adam domin rayuwa.”
Ya ƙara da cewa, harshen da masu garkuwar ke amfani da shi ya bambanta da na Fulani na Nijeriya, abin da ya ƙara masa tabbacin cewa ba ’yan cikin gida ba ne.
Sai dai ya ce, duk da haka, ana danganta Fulani gaba ɗaya da laifukan garkuwa da mutane, abin da ya kira rashin adalci ga mutanen da ba su da hannu a aikata laifi.
A cewarsa, “Dukkan waɗannan mutanen da ake kira Fulani ba Fulani na Nijeriya ba ne. Fulani daga Chadi ne. Na ga kusan su shida, babu ɗan Nijeriya a cikinsu.”
Ya kuma bayyana cewa akwai wani mutum da ba ya tare da su kai tsaye, amma ke ba su umarni ta waya a harshen Hausa, wanda ya kira “shugaban su.”
Baya ga haka, ya ce ’yan bindigar sun kuma sace wasu ’yan ƙasar China a lokacin da yake tare da su, sannan daga bisani aka sake su bayan an biya kuɗin fansa.
Wani abin da ya ƙara tayar da hankali, kamar yadda ya bayyana, shi ne yadda masu garkuwar ke kiran waɗanda suka kama da “dabbobi” yayin tattaunawa da iyalansu kan kuɗin fansa.
Ya ce, “Suna kiranmu dabbobi, suna cewa ba su gama sayar da dabbobin da suka kai kasuwa ba.”
Ya kuma ce an riƙa tilasta su ɗanɗana abinci kafin masu garkuwar su ci, tare da yin wasu matakan tsaro na ban tsoro da suka haɗa da tilasta musu ɗanɗana abinci don tabbatar da cewa babu guba.
Kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke nuna tausayi ga Fulani masu zaman lafiya, yayin da wasu ke cewa matsalar ta fi girma fiye da ƙabila, tana da alaƙa da cibiyoyin laifi da ke aiki a faɗin ƙasar.
A halin yanzu dai, al’umma da masu sharhi na ci gaba da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara tsaurara tsaro a iyakoki da kuma lalata dukkan cibiyoyin garkuwa da mutane ba tare da la’akari da ƙabila ba.
