Daga MOH BELO HABIB a Zariya
Sashen Shari’a da Gudanar da Hukunce-Hukuncen Farar Hula na Babbar Kotun Jihar Kaduna ya yi gwanjon wasu kadarori mallakin tsohon ɗan majalisar tarayya kuma surukin tsohon Shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari, Alhaji Mahmood Sani Sha’aban, sakamakon wata taƙaddamar bashi da ta daɗe tana gudana tsakaninsa da ɗan kasuwa, Alhaji Umar Faruk Abdullahi. Alhaji Sha’aban shine mahaifin Turad Sani Sha’aban, mijin Hanan Buhari.
An gudanar da gwanjon ne ranar Litinin, 1 ga Yuni, 2026, bisa umarnin kotu domin aiwatar da hukuncin da aka yanke kan bashin da ake bin Sha’aban.
Kadarorin da aka yi gwanjonsu sun haɗa da fili da gine-ginen da ke bayan babban gidansa da ke gaban Makarantar Sakandaren Therbow a Zariya, mai Takardar Shaidar Mallaka (C of O) mai lamba KD 3984. Haka kuma akwai wani fili da gine-gine da ke kan Plot No. 3, Churchill Road, GRA Zaria, mai Takardar Shaidar Mallaka mai lamba KD 11226.
Sauran kadarorin sun haɗa da fili da gine-ginen da ke Tulips, kusa da mahadar MTD a titin ƙueen Elizabeth, GRA Zaria, mai Takardar Shaidar Mallaka mai lamba KD 15052, da kuma kamfanin Mazari Nails Limited da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kano, mai Takardar Shaidar Mallaka mai lamba KD 6246.
Yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala gwanjon, lauyan Umar Faruk Abdullahi, Malam Abdullahi Yahaya (SAN), ya bayyana cewa abin da aka gudanar shi ne aiwatar da hukuncin kotu ta hanyar sayar da kadarorin wanda ake bin bashi. Ya ce, kotun ta bayar da umarnin ƙwace kadarori guda biyar na Sha’aban, huɗu daga cikinsu suna Zariya yayin da ɗaya ke Kano.
“Ya zuwa yanzu mun yi gwanjon kadarorin da ke Zariya, yayin da za a gudanar da gwanjon kadarar da ke Kano a wani lokaci nan gaba,” in ji Yahaya.
Taƙaddamar ta samo asali ne daga wata yarjejeniyar bashi da aka ƙulla a shekarar 2018 tsakanin Hon. Sani Mahmood Sha’aban (Dan Buran Zazzau) da Alhaji Umar Faruk Abdullahi. An bayar da bashin ne domin taimaka wa Sha’aban wajen shawo kan matsalolin da suka biyo bayan tsare shi a gidan yari a ƙasar Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), a shekarar 2018.
Bisa yarjejeniyar, Umar Faruk Abdullahi ya bai wa Sha’aban rancen dala miliyan ɗaya ta Amurka (US$1,000,000) da kuma naira miliyan 11.2, ba tare da ƙarin ruwa ko riba ba, bisa tsarin shari’ar Musulunci.
Lauyoyin Sha’aban ne suka tsara tare da shaida yarjejeniyar, yayin da ɗansa ya sanya hannu a madadinsa. Daga baya, bayan dawowarsa daga Dubai, Sha’aban ya sake sanya hannu domin tabbatar da amincewarsa da yarjejeniyar.
Bayan karɓar bashin, Sha’aban ya biya dala 290,762, amma daga baya ya ƙi biyan sauran kuɗaɗen da suka rage. ɗaya daga cikin sharuɗɗan yarjejeniyar ita ce a biya bashin cikin watanni shida, kuma da irin kuɗin da aka karɓa.
A ranar 12 ga Fabrairu, 2024, Babbar Kotun Shari’a ta 1 da ke GRA, Zariya, ta umarci Sha’aban da ya biya dala 709,238 da kuma naira miliyan 11.2 ga Alhaji Umar Faruk Abdullahi. Kotun ta kuma bayar da umarnin ƙwace kadarorin da aka jingina a matsayin lamunin tabbatar da bashin. Sai dai Sha’aban ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin tare da neman a dakatar da aiwatar da shi. Amma Babbar Kotun Shari’a ta yi watsi da buƙatar, haka ma Kotun ɗaukaka ƙara ta Shari’a ta Kaduna.
Daga bisani ya sake garzayawa zuwa Sashen ɗaukaka ƙara na Babbar Kotun Jihar Kaduna, inda shi ma ya sha kaye.
A ranar 29 ga Satumba, 2025, kotun ta tabbatar da hukuncin da ƙaramar kotun ta yanke. Kwafin hukuncin da ke cikin shari’a mai lamba KDH/Z/12A/2024 ya nuna cewa kotun ta umarci Sha’aban ya biya dukkan kuɗaɗen da aka yanke masa cikin naira da dala ga Babban Magatakardar Babbar Kotun Jihar Kaduna.
Kwamitin alkalan da Mai Shari’a Bilkisu Mohammed da Mai Shari’a Nana Fatima Mohammed suka jagoranta ya bayyana cewa babu wani hujja da ke nuna cewa wanda ya samu hukunci ba zai iya mayar da kuɗin ba idan ɗaukaka ƙarar ta yi nasara.
Kotun ta ce: “Babu wani abu a gabanmu da ke nuna cewa wanda ake ƙara ba shi da hali kuma ba zai iya mayar da kuɗin hukuncin ba idan ɗaukaka ƙarar ta yi nasara.”
Alƙalan sun jaddada cewa kotuna ba sa son hana wanda ya yi nasara a shari’a cin moriyar hukuncin da ya samu.
A halin yanzu, Umar Abdullahi ya samu izini daga Babbar Kotun Jihar Kano, domin aiwatar da hukuncin da aka yanke. Daga cikin kadarorin da za a yi gwanjonsu akwai gida da ke lamba 48, Yusuf Road, kusa da Hadejia Road, Bompai, Kano, wanda aka jingina domin tabbatar da bashin.
Sashen Sheriff da Gudanar da Hukunce-Hukuncen Farar Hula ya sanya ranar 13 ga Yuni, 2026, domin gudanar da gwanjon wannan kadara bisa umarnin Mai Shari’a Faruk Lawan Adamu.
