Barazanar harin Boko Haram ta hana Sallar Juma’a a Kamaru

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rahotanni daga ƙasar Kamaru sun ce barazanar kai harin mayakan kungiyar Boko Haram a garin Garwa ta yi sanadin hana gudanar da Sallar Juma’ar da aka saba a yau.

Lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin zaman dar-dar da kuma karfafa jami’an tsaro a yankin.

RFI Hausa t ruwaito cewa, bayanan sun ce tun da safe aka yi ta yaɗa labarin shirin kai harin ƴanta’addan, waɗanda suka zafafa hare-harensu a ƴan kwanakin nan.

Hakan ya sa shugabanni suak ɗauki matakin dakatar da Sallar Juma’ar domin kare lafiyar al’umma.

Cikin manyan Masallatan da aka rufe har da na tsohon shugaban ƙasar, Ahmadu Ahidjo.

Wakilin gidan jaridar, a yankin, Rilwanou Shehu Ousmane ya tabbatar da aukuwar lamarin.

By Babaji