Kungiyar Barcelona ce kan gaba a yawan zura ƙwallaye a raga a kakar nan mai 59 kawo yanzu, bayan da aka kammala wasannin sati na 21 a ƙarshen mako.
A ranar Lahadi Barcelona ta caskara Valencia da cin 7-1 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da suka kara.
Waɗanda suka ci wa Barcelona ƙwallayen sun haɗa da Frenkie de Jong da Ferran Torres da Raphinha da Fermin Lopez da ya ci biyu da Robert Lewandowski da kuma Cesar Tarrega da ya ci gida.
Sai dai Valencia ta zare ɗaya ta hannun Hugo Duro, bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu a fafatawar.
Kenan Barcelona ta ci ƙwallo 59 kawo yanzu an zura mata 24, mai maki 42 a mataki na ukun teburi kakar bana.
Real Madrid ce ta biyu da ta ci ƙwallo 50 aka zura mata 20, mai maki 49 ta daya a kan teburin La Liga.
Villareal ce ta uku mai ƙwallo 39 aka zura mata 32 a raga mai maki 34 ta biyar ɗin teburin bana.
