Neymar ya soke kwantiraginsa da Al-Hilal ta Saudiyya

Spread the love

Kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya da ɗan wasan Brazil Neymar sun amince su kawo ƙarshen kwantaragin ɗan wasan.

Neymar, mai shekara 32 a duniya ɗan asalin ƙasar Brazil ya je Al-Hilal ne a watan Agustan shekarar 2023 kan kuɗi Yuro miliyan 90, sai dai sau bakwai kacal ya buga wa ƙungiyar wasa sanadiyyar rauni da ya addabe shi.

A kakar da ke ci sau biyu kawai Neymar ya buga wasa, na baya-bayan shi ne lokacin da aka yi canji da shi a watan Nuwamba.

Ana alaƙanta shi da komawa ƙungiyarsa ta asali, wato Santos, da ke Brazil.

“Kungiyar ta gode wa Neymar kan gudumawar da ya bayar a lokacin zaman shi a Al-Hilal, kuma tana masa fatan alkhairi a nan gaba,” inji ƙungiyar.

By ukarofi