Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau
An shawarci masu yiwa Ƙasa hidima a Jihar Zamfara da su mutunta al’adun al’ummar da suke zaune tare su da yin amfani da lokacin hidimar Ƙasar wajen samar da wani tsaro mai ma’ana ga rayuwar al’ummar jihar.
Darakta-Janar na NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed, ya ba da wannan shawarar a ranar Asabar a lokacin da yake jawabi ga mambobin Batch C Stream II na 2024 dake karɓar horo yiwa ƙasa hidima a Gusau .
Shugaban masu yi wa kasa hidima na ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan maƙasudin shirin shi ne ƙarfafa haɗin kai a tsakanin matasa.
Ya buƙaci masu yiwa Ƙasa hidimar dasu kasance masu ɗa’a, don cigaban jihar Zamfara.
Janar Ahmed ya kwaɗaitar da su zauna a wuraren aikinsu kuma su dena tafiye-tafiye don kariyar lafiyar su.
