
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ƴan sanda a Abuja, ta yi watsi da rahotannin da ke cewa Laftanal Ahmed Yerima na Rundunar Sojin Ruwa ya tsallake rijiya da baya bayan wani hari da aka kai masa a Birnin Tarayyar, tana mai bayyana rahoton a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma.
Rahotannin, waɗanda aka baza su ta kafafen sadarwa a ƙarshen mako, sun yi zargin cewa wasu motocin Hilux biyu marasa lambobi sun bi diddiginsa a yammacin ranar Asabar.
A cewar rahoton wanda ba a tabbatar da ingancinsa ba, al’amarin ya faro ne tun da misalin ƙarfe 6:30 na yamma a kusa da gidan man NIPCO da ke yankin Gado Nasco a Kubwa. An ce Yarima ya tsere wa harin ne ta hanyar amfani da wata dabara.
Saidai, a sanarwar da rundunar ƴan sandan ta fitar a safiyar yau Litinin, ta ƙaryata labarin inda ta ce kwatakwata babu rahoton faruwar haka ga hukumomin tsaro a ko’ina a Abuja.
Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh a sanarwar, ta kirayi al’umma da su ƙaurace wa zancen wanda ta kira da ƙanzon kurege da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da su.
Haka kuma, ta nemi jama’a da su cigaba da kasancewa masu lura da sanya ido akan ababen da ke kai-kawo a yankunansu tare da aika wa rundunar dukkan wani abin zargi da suka gani.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da wani faifan bidiyo ya karaɗe kafafen yaɗa labarai, inda aka ga yadda Ministan Abuja Nyesom Wike yake taƙaddama da matashin sojan a wani fili.
