Op-Ed: Rasa rayuka a hanyoyinmu: Kira don tunatarwa da tallafawa – Majalisar Ɗinkin Duniya

Spread the love

Daga MOHAMED MALICK FALL da SHEHU MOHAMMED

A kowace rana rayuka suna salwanta wanda hakan ke haifar da barin iyalai cikin wani mumunan hali. Kullum bala’i na faruwa akan hanyoyinmu, cikin garuruwa masu kusa da mu. Yara, matasa, iyaye, maƙwabta sun tafi har abada.

Wannan ba hasara ba ce ta yau da kullum, annoba ce ta baƙin ciki. Wani ɓoyayyen rikici ne da ke kawar da miliyoyin rayuka a kowace shekara.

Rahoton matsayin duniya na WHO na 2023 game da lafiyar hanya ya nuna cewa hatsarin titina na kashe kusan mutane miliyan 1.19 tare da raunata kusan mutane miliyan 50 a duk shekara.

A Afirka, zirga-zirgar ababen hawa ita ce kan gaba wajen samun mace-mace tsakanin matasa masu shekaru 5-29, tare da masu tafiya a kafa da masu keke a cikin mafi rauni. Kowace lamba ba ƙididdiga ba ce kawai; rayuwa ce, labari, alkawari ne wanda bai cika ba.

A wannan Ranar Tunawa da Mutuwar Mutane akan hanya ta Duniya, mu dakata, mu tuna, mu nuna bakin ciki. Amma tunawa bai isa ba, dole ne mu yi aiki.

A Najeriya, duk wani rai da aka rasa a kan hanya, wata baiwa ce da aka rasa ga al’ummarmu: daga matasa, iyaye, ma’aikata, waɗanda suka bar mu sanadiyyar wannan anobar.

Raunin ababen hawa na daya daga cikin abubuwan da ke haddasa mutuwar yara da matasa; shugabanni, masu kirkire-kirkire, masu fasaha, malamai, da shugabannin gobe. Idan muka rasa su, za mu rasa damar, ci gaba, da bege.

Sau da yawa ana taushe martaninmu. Dokoki ba su da ƙarfi, kuma ana ɗaukar mutuwar kan hanya da sauƙi. Ana kiran mutuwar kan hanya “hatsari” kamar dai kaddara ce kawai ke da laifi, amma mun fi sanin cewa waɗannan bala’o’i ne da za a iya hana su. Kowane rauni yana barin alamar da za ta iya dawwamar tsawon rayuwa.

Dole ne mu yarda da aikin masu ba da agajin gaggawa, ‘yan sanda, ma’aikatan jinya, da likitoci. Suna fuskantar bacin rai kullum, suna garzayawa zuwa wuraren da ake kashe mutane, suna ɗaga gawarwaki, suna ta’azantar da waɗanda suka jikkata, suna ba da ta’aziyya inda baƙin ciki ya mamaye. Su jarumai ne, amma duk jaruntakarsu, ba za su iya dakatar da hatsarin kan hanya ba.

A wannan Ranar Tunawa ta Duniya, tana kiran mu da Mu Tuna. Mu Taimako. Mu kwana Muna tunawa da rayukan da aka rasa. Muna tallafa wa waɗanda aka bari a baya—iyalai, waɗanda suka ji rauni, da kuma al’ummai. Muna aiki da gaggawa, da tausayi.

Aiki yana farawa da wayar da kan jama’a. Dole ne kowane mai amfani da hanya ya fahimci cewa aminci alhaki ne na kowa. Hanyoyi ba wurin tsere tsere ba ne. Motoci ba makamai ba ne. Gudu yana kashewa. Rashin kulawa yana kashewa. Girmamawa yana ceton rayuka.

Aiki yana buƙatar tilastawa. Dokokin zirga-zirga dole ne su kasance a bayyane, masu gaskiya, kuma a yi amfani da su akai-akai.

Waɗanda abin ya shafa da iyalansu sun cancanci tallafi, kulawa, taimakon likitoci, taimakon shari’a, da kuma diyya. Zafin asara bai kamata ya zurfafa da sakaci ba.

A wannan ranar, muna girmama waɗanda suka rasa rayyukar su da wadanda suka tsira. Mun yi alƙawarin ba za mu bari basirarsu ta ɓace ba. Labarinsu zai jagorance mu; Tunawa da su zai sa mu canza.

Duk rayuwar da aka ceto nasara ce. Duk wata doka da aka aiwatar tana da ci gaba. Duk yaron da aka kare alkawari ne da aka cika. Muna da ilimi, kayan aiki, da nufin. Abin da ya rage shi ne aiki; da gaggawa, da dagewa.

Zuwa ga iyalan waɗanda aka rasa: an ga baƙin cikinku. An raba bakin cikin ku. Ba’a manta da Masoyanku ba. Tunawa da su ya zama dole a rayuwar mu.

Zuwa ga shugabanninmu: ana auna tsadar rashin aiki a rayuwa. Ku zuba jari a cikin samun lafiyar hanya. Ku karfafa dokoki. Ku gina mafi amincin tituna. Ku Ilimantar da ‘yan kasa. Kowane ma’auni yana da muhimmanci. Kowane lokaci yana da ƙima.

Ga kowane ɗan ƙasa: zaɓinku yana da muhimmanci. Gudun ku yana da muhimmanci. Mayar da hankalin ku yana da muhimmanci. Tunani na dakika ɗaya na iya ceton rayuwa.

A wannan Ranar Tunawa ta Duniya, muna sake cewa: Ku tuna. Ku taimaka. Mu yi aiki yau ba gobe ba.

Mu maida bakin ciki ya zama mafita, hasara ya zama aiki agaremu. Dole ne hanyoyin mu su sake zama inda ake tafiya a lafiya. Karda mu yarda mu sake rasa ko wani rayuwa. Dole ne a daraja rayuka. Dole ne a kebe iyalai. Tare, za mu iya sake rubuta labarin hanyoyinmu.

Ku tuna da mattatu. Ku tallafa wa masu rai. Ku yi aiki don hana ƙarin karayar zuciya. Kowace rayuwa tana da muhimmanci. Kowane iyali yana da muhimmanci.

Mista Mohamed Malick Fall shi ne mai kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya yayin da Mista Shehu Mohammed (mni) shi ne Corps Marshal/Shugaba na Hukumar Kare Haɗurra ta Ƙasa (FRSC).

By Babaji