Laftanal Yarima ya tsallake farmakin kisa a Abuja

Spread the love

A jiya Lahadi ne rahotanni suka Laftanal A.M. Yarima na Rundunar Sojin Ruwa ya tsira daga wani yunƙurin farmaki da wasu da ba a san ko su waye ba suka kai masa a Abuja.

Majiyoyin tsaro sun ce an bi motarsa ne daga wata tashar mai da ke kan hanyar Line Expressway zuwa Gado Nasco Way, inda motocin Hilux biyu marasa lamba ɗauke da mutanen da ke sanye da bakin kaya suka riƙa bin sawunsa cikin shakku.

Ganin haka ya sa Yarima ya yi amfani da dabaran tsira domin kauce wa lamarin ba tare da wata illa ta same shi ba.

Wannan lamari ya faru ne kwanaki kaɗan bayan rigimar fili da ta kunno kai tsakaninsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike, a unguwar Gaduwa, inda hotuna da bidiyo suka nuna su cikin yanayi na taƙaddama.

Wasu tsofaffin jami’an tsaro sun nuna goyon bayansu ga Yarima, suna masu cewa ba za su amince a hukunta shi ba idan ya yi aikinsa bisa doka.

Haka kuma Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya tabbatar cewa gwamnati za ta kare duk jami’in tsaron da ke aikinsa bisa doka da oda.

Hukumar tsaro ta ce bincike yana gudana domin gano musabbabin lamarin da kuma waye ya kitsa farmaki akan jami’in.

By Babaji