Super Eagles ta rasa damar shiga Kofin Duniya na 2026 bayan kaye a hannun Kongo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Super Eagles ta Nijeriya ta rasa damar shiga gasar Kofin Duniya na 2026 da za a yi a ƙasashen Kanada, Amurka da Mexico.

Jaridar NewsPointNigeria ta ruwaito cewa hakan na zuwa ne bayan da ƙasar DR Kongo ta doke ta a zangon buga fenareti a jiya Lahadi a wasan ƙalubale da suka fafata.

An tashi wasan ne 1 da 1 bayan ƙarin lokaci na zango na biyu, lamarin da ya tilasta wa ƴan wasan buga fenareti, inda Kongo ta doke Nijeriya da ci 4 da 3 wanda ya ba ta damar buga wasan neman gurbi kai tsaye a gasar a watan Maris na shekara mai zuwa.

A kwanaki kaɗan da suak gabata ne Nijeriya ta lallasa Gabon da ci 4 da 1, wanda ya ba ta damar kai wa wannan zangon.

Yanzu Nijeriya za ta mayar da hankali a wasanta na gasar Kofin ƙasashen Afirka a watan Disamba, wanda za a yi a Moroko.

By Babaji