Shin akwai ra’ifin hadisi a cikin Sahihul Bukhari?

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Wannan ce tambayar da na ci karo da ita a majalisin limamin masallacin Al-Furqan, Dr Bashir Aliyu. Tashin farko ya fara bayar da amsar cewa babu ra’ifin hadisi a cikin Bukhari, amma idan wani na ganin da akwai, to, ya kawo. Sannan ya ɗora da cewa, shehin malamin hadisi, Al-Juwayni, wanda aka fi sani da Imamul Haramain, ya ce, idan wani ya rantse akwai hadisi ra’ifi a Bukhari, to matarsa ta saku sakamakon wannan furuchi. Wannan Makala zata yi nazarin wannan da’awa.

Jamhurun Musulmin Duniya, idan ban da ‘yan Shi’a da mabiya Qur’ani zalla, duk sun yi ittifakin cewa littafin Sahihul Bukhari shine littafin na biyu mafi inganci bayan Al-Qur’ani. Ta kai baya ga ganin cewa littafin Sahihul Bukhari ba shi da wani nakasu, akwai kuma malaman da ke ganin cewa akwai hadisai da ke ciki da ka iya soke aya ta Qur’ani kan sa. A duniyar Musulunci a yau, a bayyane ya ke karara yadda hadisi ya fi Qur’ani tasiri a rayuwar Musulmi da tsarin shari’a. Duk da cewa sama da shekara dubu Imam Al-Shafi’i ya ja kunnenmu da cewa “Allah ya sanya cewa babu wani littafi da ba shi da nakasu banda littafinsa mai tsarki” a matsayin martini ga masu ganin cewa sahihayn basu da wata miskila.

Shi littafin Bukhari an wallafa shi kimanin shekarun 230 bayan wafatin manzon Allah kuma a tsawon wadannan shekaru 1200 tun daga wallafa shi zuwa yanzu, an sami mutane daban-daban wadanda ba su yarda da ingancin wasu hadisan da ke ciki ba. An fara samun wadanda ba su yarda da wasu hadisai da ke cikin Sahihul Bukhari ba tun zamanin Bukhari na raye, domin mutum na farko da ya ki karbar hadisan Bukhari shine abokin aikinsa na tattara hadisi, wato Imam Muslim, wanda ya yi zamani daya da Bukhari amma ya yi watsi da wasu hadisai da dama da Bukhari ya ruwaito wadanda bai yarda da ingancinsu yadda zai saka su a cikin na shi Sahihin ba (zan kawo misalinsu nan gaba). Sannan shekaru 50 kacal da rasuwar Bukhari, wani shehin malamin hadisin, Al Daraqutni, ya soki hadisan Sahihin na Bukhari. A cikin littafinsa Kitab al-Tatabbu’, Al Daraqutni, ya soki hadisai 217 tsakanin hadisan da Bukhari da Muslim su ka ruwaito, duk da cewa sukar ta sa, ba a kan mattanin (gundarin hadisin) ba ne amma a kan isnadi ne (wato jerin maruwaita zuwa ga annabi). A daidai lokacin da malaman hadisi su ka fara rubuta hadisai a littafai, wato a farkon karni na uku bayan hijira, babban abinda su ka fi maida hankali a kai shine wajen ingancin wadanda su ka ruwaito hadisi (Isnadi) fiye da abinda hadisin ke Magana a kai (Mattani). Wannan tsari na ingancin Isnadi shi Al Daraqutni ya nuna cewa akwai nakasu da dama cikin hadisai a Sahihul Bukhari wadanda sun kai 98. Ingancin isnadi ba ya cika sai ya dangana da annabi ba tare da katsewa ba kuma sannan ba’a sami wani cikin jerin maruwaitan na da nakasu ba, ko an taba samunsa da yin karya ko kuma raunin hadda.

Ibn Hajar al-Asƙalani, cikin Tahdhibut-Tahdhib, mujalladi na III, shafi na 509-511 ya ce “Lokacin da Bukhari ya gama rubutun sahihinsa ya kaiwa malaman hadisi irinsu Ahmad Ibn Hanbal, Yahya Ibn Main, Ali Ibnul-Madini da wasunsu domin su duba. Sun ce duk hadisansa ingantattu ne banda guda 4”. Wannan ma wata shaida ce cewa akwai hadisai masu rauni cikin Bukhari. Imam Ghazali cikin littafinsa Al-Qanun al-kulli fit ta’wil da ke bada amsar tambayoyi ya kawo wasu hadisai kamar wanda ke cewa “Shaidan na yawo cikin jiki kamar yadda jini ke yawo” (Mujalladi na 8, littafi na 73 hadisi na 238) da kuma “Abincin shaidanu shine kashin dabbobi da ƙashi” (Mujalladi na 5 Littafi na 58 hadisi na 200) a matsayin hadisan da ya ke tantamarsu cikin Bukhari.

A baya-bayan nan, malaman zamani da suka soki hadisan Sahihul Bukhari sun hada da Sheikh Ibn Uthaymeen na kasar Saudia da ya soki hadisin da ke Magana a kan Annabi Isa da Dujal, Sheikh Ibn Bn Baz, Abubakar Al Baghdadi, Rashid Rida, Syed Ahmed Khan, Mohammad Iqbal, Al Khawsary da sauransu duk sun soki wasu hadisai a Sahihul Bukhari. Sannan Shugaban malaman yan Salafiyya, wato Nasirudeen Albani na Saudi Arabia, ya soke hadisai kimanin guda 83 da ke cikin Bukhari. Cikin fitattun hadisan da Albani ya soke daga Sahihul Bukhari shine na wanda Wazi ibn Aamir ya ruwaito a cikin littafin Al-Adab Al-Mufrad hadisi na 975: 

Cewa “Al-Wazi’ ibn ‘Amir ya ce, “Da mu ka iso sai a ka ce mana, ‘Ga Manzon Allah can” sai mu ka je mu ka sumbaci hannayensa da kafarsa”. 

Wannan hadisi bayan Bukhari, Abu Dawud ya kawo shi cikin Sunan din sa (Mujalladi na 4, shafi na 357 # 5225). Bayhaqi shi ma ya kawo shi cikin Sunan (7:102). At-Tayalisi ya kawo shi a Musnad dinsa. Haka ma Al-Bazzar a nasa Musnadin (3:278), sai Ibn al-Muqri wanda ya kawo shi cikin littafinsa Kitab ar-Rukhsa, (p. 80#20). Ibn Hajar ya kawo shi a Fath al-Bari (1989 ed. 11:67 Isti’dhan ch.28 #6265) Ibn Abd al-Barr ya baiwa hadisin mukamin Hassan, al-Mundhiri ma ya tabbatar da shi Mukhtasar a Sunan din sa (8:86) da cewa hadisin Hasan ne. Sai kuma Tabarani wanda ya kira hadisin da Sahihi a littafansa biyu, wato Al-Mujam al-Kabir (vol. 5, p. 275 # 5313) da kuma Al-Mujam al-Awsat (vol. 1, p. 133 # 418). Duk da yawan wadanda su ka ruwaito wannan hadisi, bai hana Albani ya soke shi ba. Amma mu gane cewa akasarin hadisan da Albani ya soka a sahihul Bukhari, hadisai ne da su ka yi karo da akidar salafanci, kamar misalin wannan hadisi, domin sumbatar kafa a wajensu tamkar sujada ya ke. Idan ba mu manta ba, hatta durkuso wajen gaida iyaye ya hadu da irin wannan fassara ta cewa tamkar shirka ne, a lokacin da Izala ta shigo arewacin Najeriya.

Idan mu ka duba zamu ga cewa Bukhari ya tattaro hadisai 600,000 wanda a cikinsu bayan tankade da rairaya, kwaya 7563 kacal ya ruwaito a sahihinsa wadanda a cikinsu idan ka cire maimaici zaka samu ba su fi 2398 ba, wato ke nan kashi daya (1%) cikin dari (100%) na abinda ya tattara ne kawai ya iya amincewa da su don sakawa cikin Sahihinsa, yayin da ya yi watsi da kashi 99% (gwari-gwari shine cewa a duk hadisi dari da Bukhari ya tattaro guda daya tak ya ke iya amincewa da shi, sai ya zubar da sauran 99). Wannan ya nuna karara cewa a farkon karni na uku bayan hijirar manzon Allah, hadisan karya ko marasa inganci su ne su ka fi yawa kuma su ka watsu cikin al’ummar Musulmi, sakamakon siyasa da ta shigo cikin al’amuran jama’a, kuma aka fara samun banbancin aƙida tsakanin Musulmi ta samuwar kungiyoyi irinsu Kharijawa, yan Shi’a, Mutazilawa da yan Ahlu Sunna. Don haka mutane na kirkirar hadisai domin cimma wata bukata ta siyasa ko akida. Wannan yanayi ya bayyana karara idan mu ka yi la’akari da bayanin Al-Khallal inda ya ke cewa “Ibn Hanbal ya zo wucewa ta wani masallaci inda wani mai wa’azi da ke amfani da hadisan karya wajen la’antar Musulmi masu ridda ya na kira zuwa ga sunna. Sai Ibn Hanbal ya ce “Wadannan masu wa’azi na da mahimmanci ga al’umma duk da cewa abinda suke ruwaitowa ba gaskiya ba ne”. Ka ga kenan Malaman wancan zamani sun bada tasu gudunmuwa wajen cusa hadisan karya cikin al’umma.

Kwan-gaba-kwan-baya da hadisi ya samu kansa a ciki na sahihanci ko akasin haka, shi kansa wata gagarumar hujja ce wadda ya kamata ta dabbaka mana matsayin Qur’ani na kasancewa ba shi da irin wannan illa saboda kariya da ya samu daga Ubangiji, kamar yadda ya fada cikin Q15:9 “Lallai mu ne mu ka saukar da Ambato (Alqur’ani) kuma lallai mu, hakika, masu kiyayewa ne a gare shi.”

Don haka wajibi ne mu dauki Qur’ani a matsayin dan sanda da zai zama na farko wajen sahihantar da hadisi ko akasin haka. Wato duk wani hadisi da ya yi karo da aya sai mu yi watsi da shi nan take. Misali, wani hadisi cikin Muslim (Littafi na 39 hadisi na 6707) inda ya bada labarin Allah ya yi halitta a kwana bakwai wanda ya yi karo da ayoyin Qur’ani da Allah ke cewa Q25:59 “Wanda ya halitta sammai da kasa da abinda ke tsakaninsu a cikin kwanuka shida.”

Duk da karo da ayar Qur’ani, malamai da dama sun karbi wannan hadisi a matsayin sahihi duk da cewa akwai kuma wasu malaman da su ka soki Isnadin hadisin. To amma idan za mu rika amfani da ayoyin Qur’ani, irin wadannan hadisan ba za su kawo rarrabuwar kan malamai kan sahihanci ko akasin haka na hadisi ba.

Baya ga Qur’ani, abu na biyu da ya kamata mu dauka wajen tantance hadisi shine tabbatacciyar kimiyya, wato ilimi na hakika ko zahiri. Kimiyya ba kirkirar masana kimiyya ba ce, domin Dan Adam bai zo duniya ba, sai bayan an yi halittar duniya da abubuwan da ke cikinta (wato sama da kashi 99.5% na halitta ya kasance kafin a halicci mutum, kamar yadda cikin Sura Insan (Mutum) Allah ya ce; Q76:1 “Lallai ne wata mudda ta zamani ta zo a kan mutuum, bai kasance kome ba wanda ake ambata.”

Kuma duk wadannan halittu da Allah ya yi, a doron tsarin kimiyya ya yi su, don haka masana kimiyya aikinsu kawai shine na bincike da nazari domin gane yaya Allah ya halicci halittu masu rai da mara sa rai. Tun farkon duniya ake ruwan sama, amma kimiyya ta gano abubuwan da ke samuwa kafin ruwa sama ya sauka. Allah ne cikin Qur’ani ya umarce mu da yin nazarin kimiyya cikin suratul Jathiya inda ya ce Q45:3-5 “Lallai ne cikin sammai da kasa akwai ayoyi ga masu Imani. Kuma cikin halittarku da abin da ke watsuwa na dabba akwai ayoyi ga mutane masu yakini. Kuma da sabawar dare da yini da abinda Allah ya saukar daga sama na arziki, sannan ya rayar da kasa game da shi a bayan mutuwarta, da juyawar iskoki, akwai ayoyi ga mutane masu yin hankali.”

Wannan aya ta dunkule mana dukkan ilimai na kimiyya da Allah ke son mu yi, wato ilimin Astronomy da Geography, Biology, Zoology da Botany, Meteorology da Climatology da Agriculture da sauransu, kuma shine abinda ya jawo Musulmin farko su ka kafa harsashin kimiyyar da a yau muka yi barci daga barinta kuma turawa su ka dauka. Don haka wajibi mu yi la’akari da kimiyya wajen tantance hadisi. Kuma shi kansa shugaban halitta, Muhammadu Rasulillah, ya tabbatar mana da cewa wajibi mu rika amfani da kimiyya wajen tantance hadisai domin hadisi ya zo cikin Muslim (2361 littafi na 43, hadisi na 184) cewa, a lokacin farkon zuwan Annabi Madina sai ya ga manoman dabino na yin dabarar ratsa barbarar dabino da kansu, wato hada mace da namiji domin yin hakan ya fi samar da yabanya. Annabi ya hana su yin haka, sakamakon da ya jawo rashin samun yabanya. Daga baya da aka shaidawa annabi sai ya ce “Idan na umarce ku da yin wani abu bisa ra’ayina, kar ku manta ni mutum ne (wato zai iya kuskure a kimiyance)” a wata riyawar kuma ya ce “Kun fi ni sani (wato a nan yadda ilimin ratsa barbarar ya ke) a cikin ilimin da ya shafi duniya”. A nan Annabi na nuna mahimmancin ilimin kimiyya, domin ilimi ne na hakika da Dan Adam ke iya ganewa sakamakon bincike, nazari, ko yau da gobe. Duk inda aka sami irin wannan tabbataccen ilimi zai iya kore hadisin da ya ke nuna akasin haka kamar yadda annabi da kansa ya nuna mana a nan.

Abu na karshe da ya kamata ya rika taimaka mana tantance hadisi shine sahihin tarihi. Wato duk wani hadisi da aka samu ya ci karo da tarihin da ya inganta, ka san cewa wannan hadisi kirkirarre ne. Misali akwai hadisin da ya zo cewar akuya ta cinye ayar Rajamu (Hadisin Ubn Majah Kitab An-Nikah hadisi na 1944), da kuma hadisin da aka lakabawa Umar cewa su na karanta ayar Rajamu lokacin manzo (Sahih Muslim Kitabul hudud littafi na 17 hadisi na 4194). Wadannan hadisai, nakasu ne ga Musulunci kansa da sahabbai, domin ina sahabbai marubuta Qurani da mahaddata? Shin sun kasa haddace waccan aya ne ko kuwa wata makarkashiya ce a tsakanin sahabbai tun daga lokacin Sayyidina Abubakar da aka fara saka Qur’ani cikin littafi har zuwa lokacin Usmanu da aka dauki littafi guda? Ina maganar alkawarin Allah na kare littafinsa tun ya na sauka har karshen zamani? Kiristoci da Mulhidai na amfani da wannan hadisi wajen nuna cewa Qurani karya ne ba Allah ne ya saukar da shi ba, tun da har akuya ta iya cinye wani bangare.

Haka nan sahihin tarihi ya tabbatar da cewa Annabi ya yi shekaru 63 a duniya inda bayan ya kai shekarun annabta, 40, sai ya yi shekaru 13 a Makkah sannan ya yi hijira zuwa Madina inda ya kara wasu shekaru goma kafin ya yi wafati. To amma Sahihayn sun kawo hadisai masu karo da juna game da shekarun haihuwar annabi, zamansa a Makka da Madina. Bukhari ya kawo hadisai biyu (Mujalladi na 4 littafi na 56 hadisi na 747 da kuma Mujalladi na 4 littafi na 56 hadisi na 748) cewa shekarun annabi 60 (wato 40 na fara wahayi, da goma a Makka da wata goman a Madina), sannan wasu hadisan guda biyu (Mujalladi na 5 littafi na 58 hadisi na 242 da kuma Mujalladi na 5 littafi na 59 hadisi na 742) da su ka nuna shekarun annabi 63 (wato wato 40 na annabta, 13 a Makka da 10 a Madina). Hakan nan shi kuma Sahih Muslim sai ya kawo nasa hadisan cikin sahihinsa, inda guda daya ya yi daidai da Bukhari (littafi na 030 hadisi na 5795) amma dayan bai yarda da shi ba (na shekaru 63) inda nasa hadisin ya nuna shekarun Annabi 65 (cikin littafi na 030 hadisi na 5805) wato bayan shekarun annabta 40, ya yi shekaru 15 a Makka sannan ya yi 10 a Madina. Haka za ka yi ta samun hadisai masu karo da juna, misali Bukhari ya ruwaito Annabi ya yi fitsari a tsaye (Hadisi na 2471) shi kuma Ibn Majah ya ruwaito Annabin ya hana Umar yin fitsari a tsaye (Hadisi 308).

Sannan shahararren hadisin na 8 cikin Arba’una Haith na Al-Nawawi da na Muslim (Mujalladi na 22, Littafi na 1, hadisi na 36) sun ruwaito cewa an umarci Annabi ya yaki mutane har sai sun yi Imani sannan rayukansu su ka tsira. Wannan hadisi ya yi karo da ayoyin Qur’ani da dama sannan kuma ya yi karo da sahihin tarihi domin mun ga yadda Annabi ya zauna a Madina cikin yarjejniya da Ahlul Kitabi (Kamar yadda Ibn Ishaq ya ruwaito cikin Sirah da kuma hadisin Bukhari Littafi na 96 Hadisi na 36 wanda Sayyidina Ali ya yi nuni da yarjejiniyar). Hakika annabi bai hana Yahudawan Madina zabin yin addininsu ba, kuma bai kore su ba sai bayan sun karya yarjejeniyar da su ka shiga da shi, kuma a mabanbantan lokuta cikin wasu shekaru domin ya fara da korar Yahudawan Banu Qainuqa bayan Yakin Badar, sannan Banu Nadir da kuma Banu Quraiza a karshe bayan yakin Khandaq. Sannan kuma mutanen Makka bai yake su ba sai da aya ta sauka ta umarnin a Yake su.

Q22:39 “An yi izini (na yaki) ga wadanda ake yakar su da cewa lallai ne an zalunce su.”Hakika mishkiloli da suka shigo cikin hadisai da tattara su na ɗaya daga cikin abinda ya ke kawo tarnaki ga Musulmi ta fuskokin zamantakewa, aƙida da aiwatar da Musuluncin kansa yadda Allah ya umarta. Hadisai a yau sun maida ayoyin Qur’ani kujerar baya. Musulmi ya kamata su dauki saka Qur’ani gaba (amma ba irin na mabiya Qur’ani zalla da ke cewa a kori hadisai gaba daya ba), ya zama dai shine ma’auni na farko wajen tantance sahihanci ko akasin haka na hadisi. Sannan a yi amfani da ilimin kimiyya da sahihin tarihi wajen tantancewar, yin haka zai rage mishkiloli da ake fuskanta wajen aiwatar da Musulunci da hadin kan Musulmi. Kuma kada mu manta da shawarar da Imam Al-Shafi’i ya baiwa Musulmi sama da shekaru dubu da su ka wuce da cewa ““Allah ya sanya cewa babu wani littafi da ba shi da nakasu banda littafinsa mai tsarki”. Sannan mu yi riko ga umarnin Allah cewa; Q3:103 “Kuma ku yi riko ga igiyar Allah gaba daya, kuma ka da ku rarraba.”

By ukarofi