Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bankin Standard Chartered ya sanar da cewa daga ranar 28 ga Fabrairu, 2026, ba zai ci gaba da mu’amala da abokan hulɗar da ba su da aƙalla Naira miliyan 7.5 a cikin asusunsu ba — bisa wani sabon tsari da bankin ya ƙaddamar mai suna ‘Emerging Affluent Segment’.
A wata sanarwa mai taken “Muhimmin Sanarwa: Sauye-sauye a Rassa da Tsarin Hulɗar Abokan Ciniki,” bankin ya bayyana cewa asusun da ba su kai wannan ƙa’ida ba za a rufe su kai tsaye daga ranar da aka ƙayyade.
Bankin ya bayyana cewa ya cire sashen ‘personal banking’, wanda yawancin masu asusu ke ciki, tare da gabatar da tsarin ‘Assets Under Management (AUM)’ — wanda ke buƙatar abokin ciniki ya riƙe aƙalla Naira Miliyan 7.5 a bankin.
Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa daga ranar 15 ga Janairu, 2026, za a rufe wasu daga cikin rassan bankin, a wani mataki na daidaita tsarin aiki da rage farashi, tare da ƙarfafa amfani da sabbin hanyoyin fasaha.
“Rufewar rassa na daga cikin ci gaban da muka fara shekaru da suka wuce na sauƙaƙa ayyukanmu, da inganta hanyoyin sadarwa, kayayyaki da sabis, tare da amfani da albarkatu yadda ya dace domin gamsar da buƙatun abokan ciniki masu ƙaruwa,” inji sanarwar.
