Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shahararren lauya kuma masanin tattalin arziki, Dokta Olisa Agbakoba (SAN), ya bayyana wani shirin sauyi na dogon lokaci da zai iya haɓaka darajar tattalin arzikin Nijeriya zuwa fiye da naira kwadriliyan 1.5 cikin shekaru goma zuwa goma sha biyar masu zuwa, idan aka aiwatar da shi yadda ya dace.
A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Ministan Kuɗi kuma Mai Tsara Tattalin Arziki, Agbakoba ya yi kira ga gwamnati ta faɗaɗa damar samun bashi, ta ƙarfafa ingantaccen aikin gona na zamani, tare da yin gyaran dokar amfani da aasa (Land Use Act) domin buɗe sabbin hanyoyin bunƙasa arziki.
Ya yaba da matakan gwamnatin yanzu wajen ƙarfafa tattalin arzikin cikin gida, rage hauhawar farashi, daidaita musayar kuɗi, ƙara adadin ajiyar waje, da inganta samar da mai, yana mai cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta gina “tushen da zai dawo da amincewa a tattalin arziki” da rage dogaro da dalar Amurka.
Agbakoba ya ce gyaran tsarin mallakar ƙasa zai taimaka wajen sauya kadarorin da ba su da amfani a yanzu su zama dukiyar da ake iya jingina wa bashi. Ya bayyana cewa idan gwamnati ta tabbatar da tsarin mallakar ƙasa da hujjar doka, za a iya amfani da ƙasa ko gida a matsayin jinginar da bankuna za su karɓa cikin amincewa, wanda zai ƙara yawan masu samun lamuni.
Ya ce, “Wannan tsari zai fitar da kuɗin da ke maƙale a ƙasa da kadarori, ya maida su jari da zai riƙa zagayawa cikin tattalin arziki. Hakan zai ƙara likitanci a kasuwa — mutane da kamfanoni su fi samun lamuni, kadarori su zama kayan kasuwanci, kuma arzikin da ke kwance ya koma aiki.”
Masanin dokar ya kuma bukaci gwamnati ta faɗaɗa tattalin arzikin bashi da haɓaka aikin gona ta amfani da injuna na zamani, yana mai cewa hakan zai ƙara yawan amfanin gona, rage asarar bayan girbi, kuma ya tabbatar da isasshen abinci a cikin gida, tare da mayar da Nijeriya ƙasar da ke fitar da kayan gona zuwa ƙasashen waje.
“Idan muka koma daga aikin gona na gargajiya zuwa na zamani, za mu ƙara yawan amfanin ƙasa, mu rage shigo da kayan abinci daga waje, wanda hakan ke janyo hauhawar farashin dalar Amurka. Wannan mataki shi ne mabuɗin ƙarfafa naira ta fuskar tattalin arziki,” inji shi.
Agbakoba ya ƙara da cewa, duk da cewa aikin yana da wahala, zai iya yin tasiri mai ɗorewa kamar yadda aka ga nasarar gyaran tsarin haraji da gwamnatin ke aiwatarwa.
Masana sun ce wannan tsarin da Agbakoba ya gabatar na iya sake fasalta tafiyar tattalin arzikin Naijeriya, sai dai sun gargaɗi cewa matsalolin hauhawar farashi da aiwatar da shirin su ne manyan ƙalubale da za a fuskanta.
