An bayyana kansilan mazaɓar Fagolo dake ƙaramar hukumar Bichi, Hon. Habibu Musa Habibu kuma sakataren ƙungiyar Kansiloli ta Jihar Kano, a matsayin jajirtacce bisa tsayin daka da yake yi wajen cigaban al’umar yankinsa.
Ɗaya daga cikin matasan yankin Mazabar Fagolo, Aliyu Abdullahi Ibrahim, ya bayyana ayyukan kansilan da suka ƙunshi gyaran makarantu; Fagolo firamare, Kungu firamare da suka haɗa da samar da ajujuwa, zuba kujeru, saka silin, fenti, kofofi da kuma ofishin malamai.
Haka a garin Kadage da Tukwibi ya samar da kyakkyawan yanayi irin wannan a makarantunsu na firamare domin inganta ilimin al’ummar yankinsa.
“Idan ka gyara gini dole ka nemo ɗalibin da zai zo ya yi karatu a wajen, kuma dole ka samar da malamai, dukkanin mazaɓar Fagolo makarantunmu muna da malamai dai-dai ne, nan cikin hedikwatar mazaɓa ne muke da malami biyu daga hedimasta sai malaminsa, amma zuwa yanzu muna da malamai guda shida a cikin wannan makaranta, wanda shi honarabul ne ya ba da yanayi mai kyau aka dauke su a matsayin malaman BESDA,suka dawo suka yi jarabawa, bayan nan kuma aka tabbatar musu da ofarsu ta dindindin.”
Matashin ya cigaba da cewa, da a Fagolo idan yara sun gama firamare an yaye su, aƙalla mutum 500 ne suke tafiya karatun sakandire kullum zuwa da dawowa a kafa, tafiyar kimanin kilo mita 7, sakamakon haka da kyar mutum 20 suke iya cigaba da zuwa makaranta har su kammala sakandire, amma cikin yardar Allah a yanzu, bisa hoɓɓasa ta Hon. Habibu Musa an kai musu sakandire a garin Fagolo kuma ana nan ana ta yin karatu a cikinta.
A ɓangaren islamiyya ba a bar yankin a baya ba, inda da taimakon kansilan aka samar da malaman da suke koyar da yara ka’in da na’in, wanda a halin yanzu yaran yankin suna ta koyon rubutu da ajami baya ga Hausa da turanci, haka jama’ar gari da na tuntuɓe su batun Hon. Habibu dangane da kulawarsa a yankin, su ma sai godiya da sam barka.
“Waɗannan yara ɗalibai ko da an ce rubuta sunanka da sunan babanka da ajami za su iya rubutawa.” Malam Jamilu Sani Fagolo.
“Gaskiya yana ɗaukar yara mata ma yana sa su a makaranta, yana mana aiki, wallahi mun gode da wannan ƙoƙari da yake yi.” Na’ima Nasiru Fagolo.
Dagacin yankin, Malam Habibu Adamu Sarkin Fulanin yankin, ya tabbatar da aikace-aikacen da Habibu Musa Habibu ya yi a wannan mazaɓar ta Fagolo.
“Akwai abubuwa daban-daban na alamun cigaba; akwai batun kawo hasken wutar lantarki ta sola wanda shi ma an zo an duba inda za a yi tasha ta hasken wutar lantarkin.”
