Ƙaramar hukumar Bichi ta samu yabo daga kwamitin kula da ingancin ayyukan gwamnati (CRC) na jihar Kano bisa yadda ta gudanar da rabon tallafin jarin naira dubu 50 ga mata a yankin kamar yadda jami’ar yaɗa labarai Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar.Shirin na daga cikin manufofin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf na ƙarfafa tattalin arzikin mata a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Yabon ya fito ne daga bakin sakataren tsare-tsare na kwamitin, Malam Tijjani Ali Bichi, wanda ya wakilci shugaban CRC na jiha, Alhaji Usman A. Gezawa, bayan kammala rabon tallafin ga mata 80 a yankin a karo na takwas. Haka kuma, wasu mata 20 daga ƙaramar hukumar sun kasance cikin waɗanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ke ba tallafi kai tsaye a gidan gwamnatin Kano a kowane wata.
Malam Tijjani Ali Bichi ya ce Bichi ta zama abin koyi ga sauran ƙananan hukumomi saboda yadda aka gudanar da aikin cikin tsari, gaskiya da bin ƙa’ida. Ya bayyana cewa an tabbatar da tallafin ya isa hannun duk waɗanda aka tantance ba tare da wata matsala ba, lamarin da ya sa aka yaba wa shugabannin yankin kan yadda suka aiwatar da shirin.
Da yake jawabi, shugaban yankin Bichi, Alhaji Hamza Sule Maifata, ya gode wa Allah bisa nasarar da aka samu wajen gudanar da aikin. Ya ce an tsara komai yadda ya kamata, inda aka tattara cikakkun bayanan waɗanda suka amfana da suka haɗa da sunaye, lambobin NIN da lambobin waya domin tabbatar da gaskiya da kuma sauƙaƙe adana bayanan shirin domin amfani a gaba.
A nasa ɓangaren, shugaban CRC na yankin, Malam Bello Gambo Ɗanzabuwa, ya bayyana cewa tun farkon fara shirin an riga an tallafa wa mata 800 a ƙaramar hukumar Bichi. Ya ce baya ga rabon kuɗaɗen jari, gwamnati ta kuma tallafa wa mata da kaji, abincin kaji, keji da horo kan kiwon kaji, kiwon kifi, shanu da awaki, tare da wasu shirye-shiryen ci gaban al’umma kamar gyaran makarantu da samar da kayan makaranta.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Kano ta umarci a sake tattara sunayen wasu mata 300 daga ƙaramar hukumar domin su ma su ci gajiyar tallafin nan ba da jimawa ba. Malam Bello ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, shugaban yankin Bichi da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Bichi bisa irin gudummawar da suke bayarwa wajen tallafa wa mata da bunƙasa tattalin arzikin yankin, yana mai cewa irin waɗannan shirye-shirye na ci gaba da kawo sauyi mai kyau a rayuwar al’umma.
