Shugaban ƙasar Amurka ya bayyana Kamala Harris a matsayin wadda zata maye gurbinsa a matsayin wadda zata yi takarar shugabancin ƙasar Amurka.
Ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya aikawa yan jam’iyyar Democrats yana mai cewa, zai janye takararsa domin ganin ya kammala wa’adin sa.
Wannan na zuwa saura watanni kaɗan da babban zaɓen da a gudanar. Kamala Harris za ta kara da tsohon shugaban ƙasar Amurka Donald Trump.
