BIDIYO: Za mu ci gaba da amfani da tsohuwar Naira a Kaduna nan da shekara 4 – El-Rufai

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ba za a daina karɓar tsohuwar Naira, N200, N500 da N1000 ba a jihar har zuwa shekaru huɗu masu zuwa.

Ya faɗi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta na zamani a ranar Laraba.

“Ina muku alƙawari, duk ɗan jihar Kaduna da ke da tsohon kudi ya ci gaba da amfani da shi, za mu amsa daga nan har shekara huɗu,” in ji shi.

Kalli bidiyon don ƙarin bayani: