Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta bayyana ɗan takarar Sanatan Zamfara ta Tsakiya ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, Ikra Aliyu Bilbis, a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanata a yankin a zaɓen cike giɓin da da ya gudana Asabar da ta gabata.
INEC ta ce Bilbis ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu mafiyawan ƙuri’u 102, 866 wanda hakan ya ba shi damar doke abokin hamayyarsa na Jam’iyyar APC, Sanata Kabiru Garba Marafa, wandavya tsira da ƙuri’u 91, 216.
Farfesa Kabiru Abdullahi na Jami’ar Tarayya da ke Gusau, shi ne ya kasance Baturen zaɓen da ya bayyana sakamakon zaɓen.