Rubutu kan kai saƙo inda ƙafa ko gaɓɓan jikin ba su kai ba – Zarah BB

“Marubuci bango ne kuma tubali a cikin al’umma”

Daga AISHA ASAS

Jihar Sakkwato na ɗaya daga cikin jihohin da ke ɗauke da ƙwararrun marubuta duk da cewa ba kasafai ake sanin su ba, wata qila hakan ba ya rasa nasaba da daidaitacciyar Hausa da suke amfani da ita, wadda ke hana a gane su da Hausa irin ta Sakwatawa, har sai dai idan su ne suka faɗa. A yau shafin adabi ya ɗauko ma ku ɗaya daga cikin jajirtattun marubuta da suka fito daga Birnin Shehu, Fatima Bello Bala, wacce aka fi sani da Zarah BB. Matashiyar marubuciya ce da ke bada gudunmawa a cigaban adabi. A tattaunawar mu da ita, za ku ji tarihin rayuwarta da irin gwagwarmayar da ta sha a harkar rubutu tare da nasarorin da ta samu, har ma da matsayin marubutun Sakkwato a duniyar marubuta. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Zarah BB:

MANHAJA: Za mu so jin tarihin rayuwarki a taƙaice.

ZARAH BB: To da farko dai ni sunana Fatima Bello Bala, wacce aka fi sani da Zarah BB. Haifaffiyar Jihar Sokoto ce, a Ƙaramar Hukumar Sokoto North local government, a unguwar Sabon Birni Area, Sokoto. Na yi nursery school a Unity comprehensive, kafin na je Primary a Blue crescent daga nan na wuce secondary school a Sultan Muhammadu Macciɗo institute for Ƙur’an and General Studies duk anan Sokoto, haka zalika anan na yi karatun addinina. Inda yanzu nake karatu a Jami’ar Sokoto, Ina karantar Microbiology a shekara ta uku.

A wacce shekara ki ka tsunduma harkar rubutu?

Na fara harkar rubuce rubuce na, a shekarar 2014 /2015.

Za mu so ki kai mu zuwa lokacin da ki ka rubuta labarinki na farko?

Kasancewar rubutu yana ɗaya daga cikin hanyoyin isar da saƙo kuma ya isa ba tare da ƙafa ko gaɓɓan jikin ka sun isa wajen ba, kamar yadda da yawan mutane suke kallon rubutu a matsayin madubin dake haska goben su, hakan ya ƙaramin ƙarfin gwiwar fara rubuta littafina na farko mai suna ‘Aminan Juna’ wanda ya fayyace abubuwan zamantakewa masu tarin yawa a ciki, tare da nuna muhimmancin riƙe amana da alqawari, inda ya gangaro ya tabbatar mana da kalmar nan ta ɗa na kowa ne, haƙiƙa Amrah da Zarah da iyayen Amrah sun taka rawar gani a cikin labarin, inda Faruk ya so zame musu ƙadangaren bakin tulu, sai dai addu’a da samun Musty a duniyar su ya yi musu katanga da kaidin Faruk, ƙarshe dai ya tashi a tutar babu.

Duk da kasancewar sa labari na farko a duniyata, amma cikin ikon mai kowa da komai sai ya samu karvuwa a wajen mutane, wanda hakan ya buɗe ƙofa tare da jan linzamin tafiyar har zuwa yanzu, inda a daidai wannan gavar babu abin da zan ce sai, alhamdu lillahi, saboda rubutu ya gama yi min komai a rayuwa, ya yi min abubuwa da yawa wanda tsayawar numfashina kawai zai sa su tsaya, daga ciki kuwa ya haɗani da mutanen da suka kasance haske da sanyi mai sanyayawa a rayuwata; Madallah da rubutu da marubuta, Haƙiƙa marubuci bango ne kuma tubali a cikin al’umma kasancewar kafin alƙalami ya zarta na takobi.

Wane ɓangare ne ki ka fi yin rubutu kansa?

Kowanne ɓangare ina rubutu a kai musamman gefen zamantakewa, soyayya da dai sauran su, ɓangaren labaran yaƙi ne kaɗai ban taɓa gwada yi ba. Kuma ba laifi saƙon mu yana isa inda muke so, sai fatan Allah ya ci gaba da ba mu ikon rubuta abin da zai amfane mu ya amfane al’ummar Musulmi ko bayan babu ran mu, kuma ayi alfahari da mu.

Zuwa yanzu kin rubuta labarai nawa?

To, na rubuta dogon labari kusan guda tara(9) sa’annan na rubuta labarai na shiga gasa da na haɗin gwiwa haɗe da gajerun labarai ba adadi da kuma na wayar da kan al’umma a fannoni daban daban, misali a shekarar 2020 na rubuta labari na gasar muhalli wanda Bankin Bada Lamunin Gidaje na Mortgage a ƙarƙashin jagorancin Arch. Ahmed Musa Ɗangiwa, kuma labari na mai suna ‘Alaƙaƙai’ yana daga cikin labaran da suka yi nasara aka buga su a littafin ‘Muhalli Sutura’.

Haka zalika a shekarar 2022 na shiga gasar Mun Gani a Ƙasa ta Dr Dikko Radda wanda Injiniya Sirajo ya ɗauki nauyi, inda na yi rubutu akan muhimmancin zaɓen shugaba na gari mai ilimi kuma wayayye cikin ikon Allah labarina mai suna ‘Rawar Gani’ shi ne ya zo na ɗaya kuma an buga shi a cikin jerin labaran da aka wallafa a cikin littafen mai suna ‘Mizani’. Haka zalika a lokacin yajin aikin malaman jami’a, ban yi ƙasa a gwiwa wajen ci gaba da rubuce rubuce musamman akan zamantakewa da dogaro da kai.

Ita wannan gasa da ki ka faɗa kin yi ta ɗaya, wadda aka yi a Jihar Katsina, za mu so ji a taƙaice, yadda ki ka samu kanki a ciki.
Na samu kaina a cikin wannan gasar ne ta hanyar ganin sanarwar buɗe da na gani a social media, inda aka faɗi ƙa’idojin shiga gasar a shekarar 2022 a ƙarƙashin jagorancin Injiniga Sirajo.

Da wanne labari ne ki ka ci wannan gasar kuma wane irin jigo aka gina labarin da shi?

Da labarina mai suna ‘Rawar Gani’ ne na shiga gasar, jigon shi ne, muhimmancin zaɓen shugaba na gari mai ilimi kuma wayayye.

Kowane lamari na duniya na tattare da ƙalubale. Za mu so jin waɗanda ki ka fuskata a duniyar rubutu?

Hakane, rayuwa ita kanta ƙalubale ce, kuma ba za a rasa shi ba a cikin komai na rayuwa, sai dai idan nasara ta fi ƙubalen yawa za ta iya danne shi; a wannan fannin sai dai mu ce Alhamdulillahi.

Nasarori fa?

Nasarori kam, mun same su kuma muna kan samun su. Kasancewar samun mutane kaɗai babbar nasara ce.

Ko akwai wani abu da ya taɓa faruwa da ke a harkar rubutu da ba za ki taɓa mantawa da shi ba?

E akwai, na samu mutanen kirki a duniyata, akwai wasu halittu da idan ba don rubutu ba ba lallai ma na isa kusa da su ba, balle har na gan su, har ya zamana muna zama mai cike da aminci da girmama juna da su ba.

Shin waye allon kwaikwayon ki a rubutun adabi?

Kai tsaye ba zan ce ga wanda nake kwaikwayo ba gaskiya, na dai san ina ƙoƙarin bin rubutun marubutan da suka fini gogewa tare da neman shawarwarin su, da kuma karɓar gyara a duk lokacin da suka yi mini.

Mu koma ɓangaren iyali. Kina da aure?

A’a ba ni da aure.

A wasu lokuta mutane daga wasu jihohi sukan ƙaryata idan aka ce Jihar Sakkwato akwai marubuta masu dama. Ko me ya sa hakan?

Akwai marubuta sosai a Sokoto, sai dai gaskiya babu haɗin kai, ga shi kuma kamar ba su ɗauki abin ‘serious’ ba; babbar damuwar kuma shi ne manyan marubutan ba sa kama hannun yaran don gina su, muna da daktoci da farfesoshi amma sai kiga wasu jahohin sun fi mu cigaba a fannin. A kwai wani abu da na kula da shi a jahar, suna raina na su, a maimakon su gina shi ya zamo, a’a sun fi son su ɗauko hayar na waje ya yi musu aikin, ba kuma don ba su iya ba, a’a ba a ba su damar ne ba.

Sanar da mu wasu daga ƙungiyoyin marubuta da suke mallakin Jihar Sakkwato idan akwai?

Akwai ƙungiya a Sokoto, sa’annan ni kaina ina da ƙungiyar da na kafa ta ‘yan Jahar Sokoto mai suna Mashahuriya Writers Association.

Bari na ɗan mayar da ke baya, kin ce rashin haɗin kai ke jan ragamar rashin tasirin marubutan Jihar Sakkwato. Ko an taɓa yin wani yunƙuri na haɗa kai abin ya ci tura?

E an taɓa yi, ana kuma kan yi, amma su kan su marubutan ba su bada goyon baya balle har a taimaka masu.

Menene burinki a harkar rubutu?

Burina a harkar rubutu shi ne, na ƙara gogewa a cikinsa fiye da yadda nake a yanzu, ina burin na buga littafan da za a yi alfahari da ni ko bayan babu raina; waɗanda al’ummah za su amfana tare da yin alfaharin wanzuwar su a duniyar su.

Wane lokaci ne ki ka fi sha’awar yin rubutu?

Ba ni da zavi, a duk lokacin da na ji ina cikin yanayin son yin rubutun to na kan yi.

Wasu na ganin kowa ma zai iya zama marubuci, matuƙar aka koya masa, ya fahimta. Shin ya abin yake?

To, ba kowa zai iya zama ba dai gaskiya, abin kamar baiwa ce kuma kowa da wacce Allah ya ba shi a rayuwa, zai iya yiyuwa wasu suna matuqar son rubutun, amma ba su da baiwar yin shi. Saboda ba a koyawa mutum ƙirƙira, sai dai a koya masa yadda ƙa’idojin rubutu, salo da dai sauran su. Idan har sai an ƙirƙira maka labari za ka rubuta, balalle sunan ka ya zama marubuci ba gaskiya, a tawa fahimtar amma.

Ko ana gadon rubutu?

E to, ba na ce ba gaskiya don ni dai ba gadonsa na yi ba, ban sani ba ko ana yi.

Ko akwai wata kyauta da aka taɓa yi ma ki a fagen rubutu da ba za ki taɓa mantawa da ita ba?
Kyautoci ma ba kyauta ba, kuma har numfashina na ƙarshe ba zan iya mantawa da su ba. Wato tsakanina da rubutu Alhamdulillahi sai sam barka, ya ja linzamin tafiya ta har zuwa inda ban taɓa tsammani ba. Allah ya ƙara ɗaukaka rubutu da marubuta alfarmar Annabi sallallahu alaihi wasallam.

Wacce shawara za ki ba wa marubuta ‘yan’uwanki na Jihar Sakkwato?

Shawarar da zan ba su ita ce, su yi haquri, su dage, su kuma jajirce tare da nacewa, nasara da kanta tana kunyar mai naci; su yi ƙoƙarin zama tsintsiya wacce take yin shara, su riqe hannun junan su don cimma burinsu, su sani cewa, munduwa ɗaya bata amo. Haɗin kan su shi zai kawo cigaban adabi.

Rubutun batsa ya zama ruwan dare, wannan ke sa wasu lokuta ake wa marubuta kuɗin goro, cewa marubuta na ɓata tarbiyya. Ko akwai wani yunƙuri da marubuta ke yi don ganin sun yaƙi masu irin wannan rubutun?

Tabbas ya zama ruwan dare kam, E ana ƙoƙarin ganin an daƙufar da su, ta hanyar lurarwa da wa’azi game da jan hankali cikin hikima, Alhamdulillahi wasun su sun fahimta, inda masu tsaurin ido a cikin su aka fara yi musu tanadin da ba na jin zai yi masu daɗi matuƙar ba su sai ta alqalaminsu ta hanyar da ta dace ba.

Mun gode.

Ni ma na gode ƙwarai.