Nasiru Idris ya zama Gwamna mai jiran gado a Kebbi

Ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya zama sabon zaɓaɓɓen Gwamnan jihar.

A ranar Lahadi INEC ta bayyana Idris a matsayin wanda ya lashen zaɓen gwamnan jihar bayan kammala zaɓen gwamnan jihar a ranar Asabar da ta gabata.

Ya lashe zaɓen ne bayan da ya doke abokin hamayyarsa na Jam’iyyar PDP, Maj-Gen. Aminu Bande (mai ritaya).