
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Juma’a ne Gwamantin Tarayya ta yi watsi da ikirarin Shugaban Kamfanin Binance, Trigram Gambaryan, wanda ya shafe watanni takwas a komar hukuma bisa zargin sa da hannu a rashawa.
A kwanan nan ne aka sako Gambaryan, wanda ɗan Amurka ne, bayan da ƙasarsa ta tsoma baki a lamarin.
A rubutun da ya wallafa a shafinsa na X, Gambaryan ya ce tsohon Shugaban Amurka, Joe Biden ya ƙi ganawa da Shugaba Tinubu ne a kwanakin baya a lokacin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya, saboda tsare shi da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ɗora laifi akan Mai bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu inda ya ce lamarin ya sa Amurka ta rage adadin ƴan tawagar Nijeriya a babban taron.
Ya kuma bayyana sunayen waɗansu ƴan majalisa guda uku da suka nemi ya ba su cin-hancin Dala miliyan 150.
Saidai, Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga al’umma da su yi watsi da zarge-zargen da ɗan Amurkan ya yi baki ɗaya.
Ministan Labarai da Wayar da kan al’umma, Mohammed Idris, ya bayyana ikirarin Gambaryan a matsayin ƙoƙarin ruɗar da al’umma da gan-gan da kuma ƙoƙarin bata suna ga jami’an gwamnati.
Ya ce gwamnati ta ƙi amincewa da tayin Dala miliyan 5 da Binance ya yi a matsayin belin Gambaryan da ƙarin alfano daga gwamnatin Amurka ga Nijeriya.
Ministan ya yi tsokaci game da zargin cin-hanci da ɗan Amurkan ya yi, inda ya ce zuwansa Nijeriya na farko ya faru ne ba bisa doka ba, kuma babu wata hukuma da ta ɗauki mataki a kai.
Ana zargin Gambaryan da wani abokin aikinsa mai suna Nadeem Anjarwalla ne da hannu a badaƙalar wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai Dala miliyan 35.