Daga USMAN KAROFI
Tsohuwar ‘yar takarar gwamna a Jihar Adamawa, Aishatu Binani, ta sanar da komawarta jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), a wani sabon mataki na siyasa gabanin zaɓen 2027. Wannan sauyin jam’iyya ya zo ne ƙasa da watanni tara bayan ta bar All Progressives Congress (APC) zuwa African Democratic Congress (ADC).
Binani ta bayyana cewa ta yanke shawarar shiga NDC ne bayan nazari mai zurfi kan kundin tsarin jam’iyyar, inda ta ce ta gano cewa jam’iyyar na da kyakkyawan tsari da kuma mayar da hankali kan manufofi. Ta kuma jaddada cewa siyasa na canzawa ne bisa ga yanayi, kuma ba za ta zargi tsohuwar jam’iyyarta ba, domin duk matakan da ta ɗauka sun kasance bisa la’akari da halin da ake ciki a lokacin.
Ta ƙara da cewa muradun magoya bayanta su ne a gaba a dukkan matakan da take ɗauka, inda ta bayyana cewa su ne suka ba da shawarar komawarta NDC. A cewarta, magoya bayanta sun riga sun yi ƙarfi a cikin jam’iyyar kafin ta sanar da sauyin nata, har ma jihar Adamawa ke da mafi yawan mambobin NDC a yanzu.
A nasa ɓangaren, jagoran jam’iyyar NDC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Bayelsa State, Seriake Dickson, ya yi maraba da Binani da magoya bayanta, yana mai bayyana jam’iyyar a matsayin mai buɗe kofa ga kowa. Ya kuma buƙaci sauran ‘yan siyasa da ke jin ba su gamsu da jam’iyyunsu ba da su shiga NDC, yana mai cewa kowa na da ‘yancin sauya jam’iyya a kowane lokaci bisa tsarin doka.
