Daga USMAN KAROFI
Wata mata da aka sace daga yankin Kasuwan Magani a ƙaramar hukumar Kajuru ta Kaduna ta dawo gida ɗauke da juna biyu bayan shafe watanni biyar a hannun ‘yan bindiga. Rahotanni sun bayyana cewa an sace matar ne tare da wasu mutane uku yayin da take kula da mahaifiyarta mai tsananin rashin lafiya.
Wani mai sharhi a kafafen sada zumunta, Reuben Buhari, ya bayyana cewa an sako matar ne kwanaki biyu da suka gabata bayan biyan kuɗin fansa. Ya ƙara da cewa ta sha wahalhalu masu yawa a lokacin da take tsare a daji, ciki har da yunwa, rashin lafiya, da kuma cin zarafi akai-akai daga hannun waɗanda suka sace ta.
Bayan dawowarta gida, an kai ta asibiti inda likitoci suka gano cewa tana ɗauke da juna biyu, wanda ake zargin ya samo asali ne daga cin zarafin da ta fuskanta a lokacin da take tsare. Rahotanni sun nuna cewa matar na son zubar da cikin, amma likitoci sun ba da shawarar a dakata saboda halin rashin karfin jikinta, inda ake buƙatar a fara kula da lafiyarta.
Baya ga matsalolin lafiyar jiki, matar na fama da matsananciyar damuwa da tashin hankali na tunani sakamakon abin da ta fuskanta. Lamarin ya sake jaddada irin wahalhalun da mata masu fuskantar satar mutane ke sha a yankin, yayin da ake ci gaba da samun irin waɗannan hare-hare a wasu sassan jihar.
