Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa Nijeriya na bukatar gaggawar samar da ingantaccen tsari da tsarin manufofi na ƙasa domin amfani da sabbin fasahohi, musamman fasahar AI, wajen ci gaban ƙasa mai dorewa.
Sanusi ya bayyana haka ne a wajen taron karo na 8 na Committee of Pro-Chancellors of State-Owned Universities in Nigeria da aka gudanar a Kano, mai taken: “Unlocking the Potentials of Artificial Intelligence: University Governance, Internationalization and Rankings.”
Ya ce ya zama dole jami’o’in Nijeriya su jagoranci samar da tsarin AI na ƙasa, yana mai jaddada cewa bai kamata makarantu su tsaya kawai ga koyarwa da bincike ba, ya kamata su shiga gaba wajen tsara manufofin da za su taimaka wa ci gaban ƙasa.
Sarkin ya kuma yi gargadin cewa Nijeriya na iya yin baya idan ba ta tashi da wuri ba, yayin da wasu ƙasashe kamar Ghana suka riga sun fara aiwatar da cikakken tsarin AI da ke mayar da hankali kan horar da matasa, tattara bayanai da sauya tattalin arziki.
Ya ƙara da cewa jami’o’i suna da muhimmiyar rawa a matsayin ginshiƙan al’umma, yana mai cewa ya kamata su shiga cikin tattaunawar ƙasa kan shugabanci, tattalin arziki da fasaha.
A nasa jawabin, shugaban COPSUN, Ayodeji Omole, ya ce taron ya mayar da hankali kan bukatar haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki domin magance kalubalen da jami’o’in jihohi ke fuskanta.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar ya wakilta, ya ce gwamnatinsa ta ba ilimi muhimmanci a matsayin ginshiƙin ci gaba, tare da zuba jari a kayan aiki, koyon zamani da bincike domin inganta jami’o’in jihar.
