An cimma muhimman manufofin kafa ACSILS cikin shekaru 50 – Garba Kabuga

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban ƙungiyar Tsofaffin ɗaliban Kwalejin Nazarin Shari’a da Addinin Musulunci ta Aminu Kano (ACSILS) na ƙasa, Alhaji Mahmud Garba Kabuga, ya bayyana matuƙar jin daɗi da farin ciki bisa cikar makarantar shekaru 50 da kafata.

Ya ce babu abin da za su ce dangane da wannan gagarumin ci gaba face godiya ga Allah, duba da yadda manufofi da dalilan da aka kafa makarantar a kai suka cika. A cewarsa, hangen nesan magabata ya tabbata, domin makarantar ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa harkar shari’a.

Kabuga ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wajen bikin cikar makarantar shekaru 50, wanda aka gudanar na tsawon kwanaki uku.

Ya ce a baya, kafin kafa wannan makaranta, ana fuskantar ƙarancin alkalai, har ta kai ga ana ɗaukar masu aikin masinja domin su zama alkalai. Amma yanzu, a cewarsa, a Jihar Kano da ma Arewa baki ɗaya babu inda za a rasa ƙwararrun alkalai, sakamakon rawar da makarantar ta taka.

“Wannan makaranta tamkar uwa ce ga sauran irin waɗannan makarantu da aka kafa a jihohin Arewa har ma da Kudancin ƙasar nan. Yanzu mafi ƙarancin shaidar ilimi da ake samu a tsakanin alkalai ita ce diploma, yayin da da dama suke da digiri da digirgir a fannin shari’a. Kusan kaso 80 cikin 100 na alkalai a Arewa tsofaffin ɗaliban wannan makaranta ne,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar tsofaffin ɗaliban, wato ACSILS, na duba halin da alƙalai, khadis, da sauran ma’aikatan shari’a suka yi waɗanda suka fito daga makarantar, tare da ƙarfafa musu gwiwa su tallafa wa makarantar da ta ba su ilimi.

Kabuga ya bayyana cewa kafin kafa ƙungiyar tsofaffin ɗalibai, makarantar ba ta samun kulawa sosai, amma cikin ɗan gajeren lokaci bayan kafa ƙungiyar, an samu gagarumin ci gaba, inda aka yi ayyuka da dama kamar gina ɗakuna, haƙa rijiyoyin ruwa na sola, gyaran ajujuwa, da sauran muhimman ayyuka.

Ya yi kira ga sauran tsofaffin ɗalibai da ke sassa daban-daban su dawo su bayar da tasu gudunmawa ta hanyar haɗin gwiwa da uwar ƙungiya ta ƙasa domin ci gaba da inganta makarantar.

Haka kuma, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ƙara tallafawa makarantar ta hanyar samar da dokoki da tsare-tsare da za su ba ta damar cin gajiyar tallafin gwamnati. Ya nuna damuwa kan yadda makarantar ke fuskantar ƙalubale, ciki har da rashin isassun ofisoshin malamai da kujeru a ajujuwa.

A ƙarshe, Kabuga ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa ƙoƙarin da take yi na gyaran makarantar, musamman aikin katangar kewaye da kuma gyaran ɗakin taro da ya ƙone. Ya ce har yanzu akwai buƙatar ƙarin ajujuwa da ofisoshi, yana mai jaddada cewa ƙungiyarsu za ta ci gaba da jajircewa domin bunƙasa makarantar.

By ukarofi