Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar kula da ƙere-ƙere da kayayyakin kimiyya ta ƙasa (NASENI) ta ƙaddamar da shirin tallafin makamashi mai ɗorewa a jihar Kano domin rage ƙarancin makamashi da inganta rayuwar al’umma.
Shirin zai mayar da hankali ne kan rarraba murhunan girki na zamani masu tsafta da na’urorin samar da hasken rana wato sola ga kimanin mutane 2,000 a matakin farko.
Da yake jawabi, Shugaban Hukumar NASENI, Khalil Halilu, ya ce shirin zai taimaka wajen rage amfani da itace, kare lafiyar mata da yara, da kuma samar da ingantaccen wutar lantarki ga gidaje da masu kananan sana’o’i.
“Wannan shiri na kawo mafita kai tsaye ga matsalolin rayuwa ta yau da kullum, musamman ta fuskar makamashi,” inji shi.
Ita ma anata jawabin Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Jumoke Oduwole, ta bayyana shirin a matsayin wani bangare na manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na bunƙasa masana’antu, samar da ayyukan yi da ƙarfafa amfani da kayayyakin cikin gida.
Ta buƙaci waɗanda za su amfana da shirin da su yi amfani da kayan yadda ya kamata domin bunkasa sana’o’insu da inganta rayuwa.
An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a Kano, inda aka bayyana cewa za a faɗaɗa shirin zuwa sauran jihohin ƙasar nan nan gaba.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin sun yi godiya ga gwamnatin tarayya tare da alƙawarin yin amfani da kayan yadda ya dace.
