NYSC ta yi martani kan mutuwar ɗan bautar ƙasa da aka ce sojoji sun kashe a Abuja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar yi wa ƙasa hidima ta matasa (NYSC) ta bayyana cewa ta fara bincike kan yadda wani ɗan bautar ƙasa, Abdulsamad Jamiu (NS/25A/2904), ya rasa ransa a yayin wani aikin soji a yankin Shagari Estate da ke Dei-Dei a Abuja.

A cikin wata sanarwa da mahukuntan NYSC suka fitar a ranar Talata, sun bayyana cewa suna aiki kafaɗa da kafaza da hukumomin tsaro domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.

Hukumar ta kuma miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayin, tare da jaddada ƙudirinta na tabbatar da tsaro da jin dadin dukkan ‘yan bautar kasa da ma’aikatanta a faɗin ƙasar nan.

Sanarwar ta ce za su ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro da na leƙen asiri domin rage irin waɗannan haɗurra da kuma inganta kariya ga ‘yan ƙasa.

“NYSC na tare da iyalan mamacin a wannan lokaci na jimami, kuma tana addu’ar Allah ya jikansa,” inji sanarwar.

Marigayin, Jamiu, yana yi wa ƙasa hidima ne a makarantar Goɓernment Junior Secondary School da ke Bakin Ado a jihar Nasarawa kafin rasuwarsa.

A baya, rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa dan bautar ƙasar ya mutu ne sakamakon harbin bindiga a yayin artabu tsakanin sojoji da ‘yan fashi da makami a Abuja.

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne a lokacin da jami’an rundunar Guards Brigade ƙuick Response Group ke sintiri na dare, inda suka amsa kiran gaggawa kan wani harin ‘yan fashi a Shagari Estate, Dei-Dei.

Sanarwar da Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Laftanar Olawuyi Odunola ya fitar, ta ce sojojin sun yi musayar wuta da ‘yan fashin, inda a cikin rikicin ne dan bautar kasar ya samu harbi wanda daga bisani ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Sai dai iyalan mamacin sun yi watsi da bayanin rundunar sojin, inda suka zargi sojojin da harbin Jamiu kai tsaye a cikin ɗakinsa.

A cewar iyalan, harbin ya same shi a kai nan take ya mutu, kuma lamarin ya faru ne a gaban ‘yar uwarsa da ke cikin gidan a lokacin da iyayensu ba su nan

By ukarofi