Birtaniya ta fitar da tsarin shirye-shiryen ziyarar Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Birtaniya ta fitar da jadawalin ziyarar Shugaba Bola Tinubu, wadda za a gudanar daga ranar 17 zuwa 19 ga watan Maris, 2026.

A cewar jadawalin, za a karɓi shugaban ne a Windsor Castle, inda zai halarci tarurrukan tattaunawa tsakanin kasashen biyu, bukukuwan girmamawa, da kuma ganawa da ‘yan Najeriya mazauna Birtaniya.

An tsara fara shirye-shiryen ziyarar a ranar 17 ga Maris, inda jami’an tsaro za su gudanar da bincike, rufe wasu hanyoyi, da kuma atisayen jerin gwanon tarba kafin isowar shugaban.

Tinubu zai isa Birtaniya a hukumance a ranar 18 ga Maris, inda Prince William da Catherine, Princess of Wales za su tarbe shi.

Bayan haka za a gudanar da bikin tarba na musamman a Datchet Road, inda za a busa taken kasashen biyu tare da duba girmamawar rundunar tsaro.

Daga nan ne shugaban zai shiga jerin gwanon keken sarauta zuwa Windsor Castle, inda Sarki Charles III da Sarauniya Camilla za su karɓe shi.

By Babaji