Bode George ya yi fatali da nasarar Tinubu, ya ce zai yi ritaya daga siyasa

Daga BASHIR ISAH

Tsohon gwamnan soji na Jihar Ondo, Bode George, ya bayyana zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisu da ya gudana ranar Asabar da ta gabata a matsayin abin kunya.

George ya ce Shugaban INEC ya gaza, bayan da ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin zai gudanar da zaɓe.mai tsabta ta amfani da na’ura, amma a ƙarshe lamari ya sauya.

Kazalika, ya ce zai yi ritaya daga harkokin siyasa bayan kammala zaɓen gwamnoni ranar 11 ga Maris.

Bode George, wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a shiyyar Kudu maso Yamma, ya bayyana nasarar da Ahmed Tinubu a matsayin duhu da ya lullube masu taya shi murnar lashe zaɓe.

A cewarsa, “Shugaban INEC ya yi wa duniya alƙawari sahihin zave kuma Shugaban Ƙasa ya rattaɓa wa Dokar Zaɓe hannu.

“Sun bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa za mu yi koyi da sauran ƙasashen duniya da suka waye game da zaɓe, inda za a tattara sakamako ta intanet.

“Na yi mamakin yadda a ranar zaɓe, ya fito yana faɗin akwai cunkushewar sadarwa a fasahar. Wannan abin kunya ne da tozartarci wanda ba a yarda da shi ba.

“Saboda Allah, sai zuwa yaushe ‘yan Nijeriya za su zama masu faɗar gaskiya? Yaushe NIjeriya za ta fita daga irin wannan shiriritar?