Man United ta sha alwashin lashe FA Cup bayan ɗaukar Caraboa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Manchester United ta mayar da hankali kan yadda za ta lashe kofi na biyu a bana, bayan ɗaukar Caraboa Cup da ta yi ranar Lahadi.

Karon farko da ƙungiyar Old Trafford ta ɗauki kofi tun bayan cin League Cup da Europa League ƙarƙashin Jose Mourinho a 2016/17.

United ta kai zagayen daf da na kusa da na ƙarshe ranar Laraba, bayan da ta ci West Ham United 3-1 a zagaye na biyar a FA Cup a Old Trafford.

Kenan United za ta kara da Fulham a quarter finals cikin watan Maris a Old Trafford.

Rabon da United mai FA Cup 12 ta lashe kofin tun kakar 2015/16, shine na ƙarshe da ta daga.

Ƙungiyar Old Trafford wadda ta lashe Caraboa Cup bayan cin Newcastle United a bana a Wembley na harin daukar kofi uku nan gaba.

Tana cikin takarar Europa League zagayen ‘yan 16, wadda za ta kece raini da Real Betis gida da waje.

Haka kuma United tana ta uku a teburin Premier League da tazarar maki biyu tsakaninta da Manchester City ta biyu.

Arsenal ta hada maki 60 ranar Laraba ta ci gaba da zama ta daya ta kuma bai wa City tazarar maki biyar tsakani, bayan wasa 25 a gasar ta Premier League.