Boko Haram sun kashe kwamandojin ISWAP 10 a yankin Tafkin Chadi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Aƙalla mayaƙan ISWAP goma, duk da manyan kwamandojinsu suka rasa rayukansu yayin artabu da abokan hamayyarsu a ta’addancin, Jama’at Ahl as-Sunnah lid- Da’awah wa’l- Jihad, wani nau’in Boko Haram na Arewa maso gabashin tafkin Chadi suka kai musu farmaki. 

Zagazola Makama, fitaccen mai bibiyar lamurran ƙungiyoyin ta’addancin ne ya bayyana hakan.

Kamar yadda ya ce, ‘yan Boko Haram na Buduma sun yi luguden wuta ga ISWAP, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mayaƙan da dama a bakin tafkin dake tsakanin iyakar kogin Kaduna da Kandahar na Jamhuriyar Nijar. 

An jefa mayaƙa da dama cikin ruwan, daga bisani ‘yan Boko Haram na Budama suka kama mayaƙan ISWAP guda 10 bayan gumurzun. 

Vanguard ta ruwaito cewa, ƙwararren da wani jami’in tsaro na tafkin Chadi sun ɗauki bidiyon dake nuna yadda ƙungiyoyin ‘yan ta’addan guda biyu suka yi musayar wuta a kan jirgin ruwa. 

Haka zalika, a bidiyon da ya ɗauki tsawon awa 6:40 wanda Zagazola ya naɗa, an kama shugabannin ISWAP guda biyu, gami da yi musu yankan rago. Babban shugaban ƙungiyar Budama, wanda ake zarginsa da zama Muhammad Ari, ƙasurgumin jagoran yaƙi, wanda ya bayyana a bidiyon, ya ce Ubangiji na cigaba da basu ikon samun nasara a kan maƙiyansu (ISWAP). 

Ya ce: “Mu ne masu jahadi daga ƙungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad na tafkin Cadi. “Sanin kanku ne, an daɗe ana bata-kashi tsakaninmu da maƙiyanmu (ISWAP) sama da watanni da suka shuɗe, kuma Ubangiji na bamu nasara wajen kauda maƙiyanmu daga doron ƙasa.

“Mun kama kusan goma daga cikinsu duk da wasu daga cikin kwamandojinsu, sannan mun tambayesu dalilin da ya sa suke yaƙarmu. Amma kwamandojin nasu sun ce basu da wani dalili, kawai dai suna yaƙarmu ne.

“To ko shugabannin ku da kuke bi a makance, sun ce ba su san dalilin da ya sa suke faɗa da mu ba, balle ku mabiyansu. 

“A fari dai, muna yin abu iri ɗaya sannan muna tafiya kan turba ɗaya kafin ku canza, gami da barin koyarwar Ubangiji, tare da aikata dukkan munanan abubuwa. 

“Saboda haka, muna tabbatar muku da cewa Ubangiji zai cigaba da bamu nasara wajen gamawa da dukkan ku daga doron ƙasa.” 

Zubda jinanai tsakanin ƙungiyoyin ‘yan ta’addan biyu na cigaba da ƙamari musamman a iyakar tafkin Cadi, Abadam, Jamhuriyar Nijar, dajin Sambisa da tsaunin Mandara tare da ritsawa da ɗaruruwan mutane, daga ɓangarorin guda biyu a shekarar da ta gabata.

“A ranar 24 da 28 na watan Maris, 2022, ‘yan ta’addan JAS masu bin bayan Bakura Buduma, sun yi kwanton ɓauna gami da sheƙe ‘yan ta’adda 45 a Yauma Wango da Ngaama, cikin Ƙaramar Hukumar Abadam na jihar Borno,” a cewar ƙwararren