Boko Haram sun kashe mutane 40 a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mayaƙan Boko Haram sun kashe farar hula 40 a Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno a Arewa maso gabashin Nijeriya.

Ƙungiyar Boko Haram su na ci gaba da ta’asa jifa-jifa duk da kassara ta da hukumomin Nijeriya suka ce sun yi.

Rahotanni sun ce ɗimbin ‘yan ta’adda ne suka yi wa farar hula da ba su ɗauke da makami ƙawanya, inda suka yi ta yi musu yankan rago a ranar Lahadi.

‘Yar majalisar wakilai ta Tarayyar Nijeriya da ke wakiltar mazaɓar, Zainab Gimba ta tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labari.

Wata majiya ta tsaro ta shaida wa jaridar Daily Trust ta ce an kashe masu sana’ar gwangwan da dama, kuma tuni aka binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Wani rahoton kuma ya yi nuni da cewa gwamman ‘yan ta’adda ne suka kai wa farar hular, waɗanda ƙananan manoma ne farmaki da takubba.

Yanzu ana nan ana laluben sauran gawarwakin waɗanda ba a gani ba a cikin dazukan da lamarin ya auku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *