Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mijin matar da aka yi wa kisan gilla tare da ‘ya’yanta huɗu a Jihar Anambra, Jibril Ahmed, ya tattara komatsansa ya bar jihar ya koma Jihar Adamawa da zama.
Haka kuma Gwamnan Jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo, ya bai wa magidancin tallafi na N500,000 domin rage raɗaɗin ibtila’in da ya auku gare shi.
Da yake yi wa manema labarai bayani, Jibril Ahmed ya ce shi ɗan asalin Adamawa ne, kuma ya ɗauki matakin komawa Adamawar ne domin ya fara sabuwar rayuwa saboda a yanzu shi kaɗai ne ya rage bayan da tsegerun IPOB suka shafe masa ahalinsa baki ɗaya
‘Yan haramtacciyar ƙungiyar ‘yan ta’adda ta IPOB, a ranar Lahadi sun kashe ‘yan Arewa 10.
Mutane goman da ‘yan IPOB ɗin su ka kashe sun haɗa da wata mata mai juna-biyu, ‘ya’yanta huɗu da wasu mutane shida a Isulo, Ƙaramar Hukumar Orumba ta Arewa a Jihar Anambra.
An bayyana sunan matar da aka kashe da Harira Jibril, mai shekaru 32, yayin da yaran huɗu kuma aka bayyana sunayensu da Fatima mai shekaru 9; Khadijah, 7; Hadiza, 5 da; Zaituna, 2.
Da yake bayyana yadda aka kashe matar tare da ‘ya’yanta, mijinta Jibril Ahmed ya shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun yi garkuwa da su ne a hanyarsu ta komawa gida bayan wata ziyara da suka kai Orumba ta Arewa.
Usman Abdullahi, shugaban al’ummar Hausawa a Ihiala shi ma ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce matar da aka kashe ‘yar asalin jihar Adamawa ce.
Ya ce ɗaukacin al’ummar Hausawa sun bar Ihiala, sakamakon hare-haren da ake kai wa waɗanda ba ‘yan asalin yankin ba.